Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 321, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,223 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikata mutum 92,981, sannan an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 11 a yankin Beit Lahiya na Gaza

Alhamis, 22 ga watan Agusta, 2024

0311 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 11 a harin da ta kai ta sama kan wani rukunin gidaje a garin Beit Lahiya da ke Gaza, in ji kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA.

Mahukunta a Tel Aviv, waɗanda aka gurfanar a Kotun Duniya kan zargin kisan kiyashi, sun kashe Falasɗinawa fiye da 40,000, galibinsu mata da yara, kana sun jikkata fiye da mutum 92,000, tun daga watan Oktoban bara.

Dubbai sun mutu a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da suka danne su, sannan dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa fiye da 10,000.

Sai dai masana sun ce alƙaluman mutanen da suka mutu sun zarta haka nesa ba kusa ba.

Amurkawa likitoci da ma'aikatan jiyya 45 da suke aikin kula da lafiyar mutane a Gaza tun daga watan Oktoba sun ce mai yiwuwa mutanen da suka mutu sakamakon kisan kiyashin da Isra'ila take yi a Gaza "sun zarta 92,000".

Wani bincike da aka wallafa a mujallar lafiya ta Lancet, ya nuna cewa yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza ya kashe mutum fiye da 186,000.

0230 GMT — Hamas da Islamic Jihad sun jaddada matsayarsu kan sharuɗɗan tsagaita wuta

Ƙungiyoyin gwagwarmaya na Falasɗinawa wato Hamas da Islamic Jihad sun jaddada matsayarsu game da sharuɗɗan da suka gindaya kan yarjejeniyar tsagaita da Isra'ila, ciki har da kawo ƙarshen hare-hare a Gaza carnage, da janyewar Isra'ila daga yankin da sake gina shi da kawo ƙarshen ƙawanyar da aka yi wa yankin da kuma musayar fursunoni.

Sun bayyana haka ne a wata sanarwa da Hamas ta fitar bayan ganawar da aka yi tsakanin Mohamed Ismail Darwish, shugaban Majalisar Shura ta Hamas, da Sakatare Janar na Islamic Jihad, Ziad al-Nakhala, da mataimakinsa Mohamed Hindi, ko da yake a a faɗi wurin da aka yi ganawar ba.

A cewar sanarwar, ƙungiyoyin biyu sun jaddada buƙatar gaggauta kai kayan agaji Gaza ba tare da la'akari da sakamakon tattaunawar ba.

#