Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 281 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,345 — galibinsu mata da yar –– sannan ya jikkata mutum sama da 88,295, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzai.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 71 da jikkata kusan 300 a wani sabon hari da ta kai Gaza

1001 GMT — Akalla Falasdinawa 71 ne aka kashe tare da jikkata wasu sama da 289 a wani harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira a kudancin Gaza.

Sanarwar Ma'aikatar Lafiya ta ba da sabuwar ƙididdigar "adadin kisan gillar da Isra'ila ta yi" a sansanin Al Mawasi, daga aƙalla 20 da ta ce da farko an kashe.

Tun da farko a cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar ta ce "gawawwakin Falasɗinawa 20 da kuma fiye da 90 da suka jikkata sun isa cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke Khan Younis bayan da sojojin Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai a yankin Al Mawasi da ke yammacin Khan Younis a kudancin zirin Gaza."

Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, sojojin na Isra'ila sun yi amfani da manyan makamai masu linzami guda biyar, wajen kai hari a yankin Al Mawasi, wanda sojojin Isra'ila a baya suka ayyana a matsayin wani yanki mai aminci.

0305 GMT — Wakilin Falasɗinu na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya Riyad Mansour ya jaddada cewa Isra’ila na ci gaba da raba Falasɗinawa da muhallansu a Gaza a kullum.

“Muna sake kira, cikin gaggawa, ga ƙasashen duniya da su dakatar da Isra’ila daga kisan da take yi wa jama’ar Falasɗinawa,” kamar yadda Mansour ya rubuta a wani roƙo da ya aika wa shugabannin duniya.

Mansour ya sake jaddada cewa “ana ci gaba da tilasata wa farar hula barin muhallansu a faɗin Gaza bisa rashin mutunci da rashin bin doka, wanda ke haifar da tarzoma da rudani, musamman ga yara da sauran fararen hula masu rauni, ciki har da marasa lafiya, da waɗanda suka jikkata da nakasassu."

2117 GMT — Kafofin watsa labarai a Isra'ila sun ambato wasu majiyoyi da ke cewa Firaminista Benjamin Netanyahu kusan shi kaɗai yake yin kiɗansa, sannan ya yi rawarsa a tattaunawar da ake yi da ƙungiyoyin fafatukar kare Falasɗinawa game da musayar fursunonin da Isra'ila ke tsare da su da kuma Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su.

Kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN ta ambato wasu majiyoyi da ba sa so a ambaci sunayensu suna cewa Netanyahu shi kaɗai yake tattaunawa da sauran ɓangarorin, kuma ya yanke shawarar ƙin sassauta ra'ayinsa.

Netanyahu ne yake jagorantar dukkan tattaunawar da ake yi, kuma ya mayar da hankali a kan tattaunawar fiye da yadda ya yi a baya, in ji majiyoyin.

Ita ma jaridar Yedioth Ahronoth ta ce ana fargabar cewa Netanyahu yana ƙoƙarin kawo cikas a game da tattaunawa kan musayar fursunonin bayan ya samu rashin jituwa da shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar Mossad, David Barnea, a kan wasu daga cikin sharuɗɗan tattaunawar.

Ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan bambance-bambancen da ke tsakanin Netanyahu da Mossad da kuma hukumar tsaron Isra'ila, Shin Bet, shi ne hukumomin tsaron ba su amince a koma fagen yaƙi ba sai idan Hamas ta keta sharuɗɗan jarjejeniyar, yayin da shi kuma yake so a ci gaba da yaƙi ko da kuwa mai zai faru.

2108 GMT — Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga Amurkawa kada su kawar da kai daga yaƙin Gaza

Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga al'ummar Amurka da kada su bari guguwar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ta kawar da hankulansu daga babban bala'in da ke faruwa a Gaza.

"A yayin da yawancin kafofin watsa labarai suka mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Amurka, dole ne mu ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Gaza, inda mutane suke ci gaba da fuskantar bala'i da rashin jinƙai," a cewar wata sanarwa da Sanders ya fitar.

Sanders ya ƙara da cewa Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Falasɗinawan Gaza ba tare da sassauci ba, yana mai zargin cewa Firaminista Benjamin Netanyahu "ya yi watsi da dukkan dokokin ƙasashen duniya sannan ya jefa rayuwar al'ummar Gaza cikin masifa".

"Shi ya sa Netanyahu yake fuskantar tuhuma daa Kotun Hukunta Manyan Laifka ta Duniya," in ji Sanders.

Sanatan wanda ke takara a matsayin ɗan indifenda ya ce Amurka tana ci gaba da kashe biiliyoyin dala don taimaka wa Isra'ila sannan tana ba ta bama-bamai da makamai don ci gaba da yaƙi a Gaza.

"Mu, Amurkawa, muna da laifi a wannan ta'asa," in ji Sanders, sannan ya yi kira ga Amurka ta daina taimaka wa "yaƙin da Netanyahu yake yi".

#