Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 77 tana yi a Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 20,000, da jikkata fiye da 52,600.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe Falasdinawa 20,057 a Gaza tun 7 ga watan Oktoba

0509 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 20,057 a Gaza tun 7 ga watan Oktoba

Adadin Faladinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 20,057, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ranar Juma'a.

An jikkata akalla mutum 53,320 a hare-haren da Isra'ila ta kai yankin tun daga 7 ga watan Oktoba, in ji ma'aikatar.

"An kashe akalla mutum 390 sannan aka jikkata mutum 734 a awanni 48 da suka gabata inda aka katse hanyoyin sadarwa na Zirin Gaza," a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

0054 GMT — An sake jinkirta kaɗa ƙuri'ar MDD yayin da Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a Gaza

Majiyoyin diflomasiyya sun ce Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sake yin watsi da kaɗa ƙuri'a kan ƙudurin da aka jinkirta kan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Dage kaɗa ƙuri'ar da aka yi a yau Juma'a ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da ta dinga adawa da shawarwari da dama a lokacin ƙudurin, ta ce a shirye take ta ba da goyon baya a yadda take a halin yanzu.

Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kaɗa ƙuri'a da aka daɗe ana jinkirtawa kan wani sabon kuɗuri na dakatar da yaƙin ta wata hanya, wadda za ta ba da damar ƙara kai agajin jinƙai.

Isra'ila na ci gaba da luguden a Gaza / Hoto: AA

0110 GMT — Mun shirya don kada ƙuri'a kan ƙudurin Gaza

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a shirye yake ya kaɗa ƙuri'a kan daftarin kudirin ba da agajin jinƙai a Gaza, in ji jakadiyar Amurka a MDD.

"Ina so in gaya muku cewa mun yi aiki tuƙuru da himma a cikin makon da ya gabata tare da ƙasar UAE da Masar, don samar da wani ƙuduri da za mu iya marawa baya. Kuma muna da wannan ƙuduri a yanzu.

"A shirye muke mu kaɗa ƙuri'a a kai," kamar yadda Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa manema labarai bayan wani taron majalisar dokoki na sirri da aka yi kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Ta ce wani ƙuduri ne da zai kawo agaji ga mabuƙata.

2155 GMT — Fiye da kasashe 20 sun shiga gamayyar kawancen hadin gwiwa na Bahar Maliya

Sama da kasashe 20 ne suka shiga cikin kawancen da Amurka ke jagoranta domin kare jigilar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya daga hare-haren 'yan tawayen Houthi na Yemen, kamar yadda Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta bayyana.

'Yan tawayen Houthi sun sha kai hare-hare kan jiragen ruwa a muhimmin titin jiragen ruwa tare da kai hare-hare na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, inda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula.

Mai magana da yawun Pentagon, Major General Pat Ryder ya shaida wa manema labarai cewa, "Mun sami sama da kasashe 20 da suka sanya hannu kan shiga cikin kawancen."

Ryder ya ce Houthis suna "kai hari ga walwalar tattalin arziki da ci gaban al'ummomin duniya," tare da zama "'yan fashi a kan babbar hanyar kasa da kasa wato Bahar Maliya."

Dakarun hadin gwiwa za su "yi aiki a matsayin sintiri iri-iri na babbar hanya, suna sintiri a Tekun Bahar Maliya da Tekun Aden don mayar da martani - da kuma taimakawa kamar yadda ya cancanta - tasoshin kasuwanci da ke jigila a wannan muhimmiyar hanyar ruwa ta kasa da kasa," in ji shi, yana mai kira ga Houthis da su daina kai hare-haren.

#