Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 319, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,139 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,743, kana an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzan gine-gine da aka rusa.
Talata, 20 ga watan Agusta, 2024
0717 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta gano gawawwaki shida na mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin ba-zata da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata ta ce ta gano gawawwakin ne a wani samame da ta kai da tsakar dare a kudancin Gaza.
Rundunar sojojin Isra'ila ba ta faɗi yadda aka kashe mutanen ba. Amma sau da dama Hamas ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe wasu daga cikin waɗanda ta yi garkuwa da su a luguden wutar ta take yi babu ƙaƙƙautawa a yankin, wanda ya mayar da kusan ɗaukacin yankin tamkar kufayi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 40,000 sakamakon hare-haren da take kai wa Gaza.
"Galibin mutanen da ta kashe mata da yara ne. Wannan babban bala'in ya faru ne sakamakon gazawar Rundunar Tsaron Isra'ila wajen kiyaye dokokin yaƙi," a cewar Babban Jami'i na MDD kan Kare Hakkin Ɗan'adam Volker Türk a wata sanarwa da ya fitar a baya bayan nan.
2033 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a Gaza a yayin da Amurka ke jan-ƙafa kan tattaunawar tsagaita wuta
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla tara, cikinsu har da yara, a wani hari ta sama da ta kai kan wani dandazn jama'a a sansanin al-Shati (Beach) da ke yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA.
"Jiragen yaƙin masu mamaya sun kai hari a wani rukunin gidaje da ke Khan Younis a kudancin Gaza," in ji kamfanin dillancin labaran.
2000 GMT — Hamas ta ce Amurka na jan-kafa kan tattaunawar tsagaita wuta don Isra'ila ta ci gaba da kisan kiyashi
Mai magana da yawun ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas Osama Hamdan ya ce ƙungiyarsu za ta yi biyayya ga shirin tsagaita wuta da a baya shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar, yana mai ƙarawa da cewa Washington na jan-ƙafa kan batun domin bai wa gwamnatin Netanyahu damar ci gaba da yin kisan kiyashi a Gaza.
Amurka tana "jan-ƙafa ne domin Israi'ila ta ci gaba da kisan kiyashin da take yi," kamar yadda Hamdan ya shaida wa Al Jazeera bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi iƙirari cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar masa zai goyi bayan shirin Amurka na tsagaita wuta a Gaza.
"Isra'ilawa sun janye daga shirin da Biden ya gabatar. Kalaman da Netanyahu ya yi game da amincewa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta sun nuna cewa Amurka ta gaza rarrashinsa domin ya amince da shirin da suka gabatar a baya," in ji Hamdan.