Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 167 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,988 tare da raunata wasu 74,188 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki.
1005 GMT — Hotunan tauraron ɗan'adam na MDD sun tabbatar da lalata kashi 35 na gine-ginen Gaza
Hotunan tauraron ɗan'adam da cibiyar tauraron ɗan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi nazari sun nuna cewa kashi 35 cikin 100 na gine-ginen Gaza sun lalace sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankin Falasdinawa.
Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a matsayin mayar da martani ga hare-haren Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan 32,000, a cewar hukumomin lafiya a Gaza.
A cikin tantancewar da ta yi, Cibiyar Tauraron Dan'Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, UNOSAT, ta yi amfani da hotuna na tauraron dan'adam da aka tattara a ranar 29 ga watan Fabrairu tare da kwatanta su da hotunan da aka dauka kafin da bayan fara sabon rikici.
An gano cewa kashi 35 cikin 100 na dukkan gine-gine a Gaza — gine-gine 88,868 - sun rushe ko kuma sun lalace.
Daga cikin wadannan, ta gano gine-gine 31,198 da aka lalata, 16,908 sun rushe baki ɗaya, sannan 40,762 sun lalace sosai.
0856 GMT — Yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 31,988
Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta bayar da rahoton cewa mutum 65 ne suka mutu a cikin awa 24 da suka gabata sakamakon hare-haren Isra'ila, yayin da wasu 92 suka jikkata.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe zuwa yanzu tun bayan fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoban bara, ya kai 31,988, yayin da yawan waɗanda suka jikkata ya kai 74,188.
Hare-haren da Isra'ila ke zafafa kaiwa Falasɗinu na ci gaba da yin mummunan tasiri a kan fararen hula a yankin Gaza.
0812 GMT — Blinken ya gana da Yarima mai jiran gado na Saudiyya don tattaunawa a kan Gaza
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya gana da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman da kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Yarima Faisal bin Farhan don tattaunawa a kan yanayin jinƙai da ake ciki a Gaza da kuma ƙoƙarin ƙara yawan agaji ga Falasɗinawa.
Blinken ya fara rangadi ne a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Laraba.