Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 426 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,538. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023.

Kai-tsaye: Harin da Isra'ila ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira a Gaza ya halaka aƙalla mutum 21

Alhamis, 5 ga Disamban 2024

1835 GMT — Wani jami'in lafiya na Falasdinu ya ce akalla mutane 21 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wani sansanin da ke dauke da 'yan gudun hijira a Gaza.

Atif Al-Hout, daraktan Asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, ya ce akalla mutane 28 ne suka jikkata sakamakon harin.

Akalla gawarwakin mutane 15 ne suka isa asibitin, amma ba a san ainihin yawansu ba, domin da yawa daga cikin gawarwakin wadanda suka mutu sun dagargaje, wasu babu wasu sassan jikinsu wasu kuma sun ƙone sosai.

Harin ya afku ne a yankin Mawasi, wani sansani da ke bakin teku da ke dauke da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu a kusa da birnin Khan Younis na kudancin kasar.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragenta sun kai hari kan yankunan Hamas, amma ba zai yiwu a kai ga tabbatar da ikirarin na Isra'ila ba.

1846 GMT — Sojojin Isra'ila sun dawo da gawar wani daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta kwato gawar Ita Svirsky wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

A wata sanarwa da kungiyar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta fitar, ta ce mayar da "gawar Itay don binne ta a Isra'ila ya bai wa danginsa wani dan saukin ƙuncin rai".

1807 GMT — Harin Isra'ila ya kashe Falasdinawa 47 a yankin

Likitocin Falasdinawa sun ce wasu hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe akalla mutane 47 a yankin.

Mazauna yankin sun ce tankokin yaki sun ci gaba da kutsawa kwana guda bayan da sojojin Isra'ila suka ba da sabbin umarnin kwashe mutane a wajen.

Yayin da harsasai suke faɗawa a kusa da wuraren zaman mutane, iyalai sun bar gidajensu inda suka nufi yamma zuwa yankin da aka keɓe a matsayin na jinƙai na Al Mawasi.

#