Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 84 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 21,320, sannan sun jikkata fiye da mutum 55,603, a yayin da kasar ke ci gaba da luguden wuta a yankunan Falasdinawa.

KAI-TSAYE: Hamas ta ce kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza yana da muhimmanci

2348 GMT — Hamas ta ce kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza yana da muhimmanci

Rundunar sojin kungiyar Hamas ta Falasdinu ta bayyana cewa kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza shi suka fi fifitawa, tare da jaddada yin watsi da duk wata yarjejeniyar musaya ko tattaunawa inda har ba a cika wannan sharadi ba.

An bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da Abu Ubaida, mai magana da yawun rundunar Al Qassam Brigades ya yi, wanda aka watsa a tashar talabijin ta Aljazeera.

Abu Ubaida ya sanar da cewa mayakan Al Qassam "sun lalata motocin soji fiye da 825, da suka hada da manyan motocin yaƙi da tankokin yaƙi tun farkon mamayar da Isra'ila ta kai ta ƙasa."

Ya ƙara da cewa: "Abin da muka sa a gaba shi ne mu dakatar da kai hare-hare kan al'ummarmu a Gaza, kuma babu wani fifiko da ya wuce haka."

Ya jaddada cewa "ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar musaya ko shawarwari ba kafin a daina kai hare-hare kan al'ummarmu a Gaza."

0128 GMT — Amurka ta yi ikirarin harbo jirgin yaki mara matuki da makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba

Wani jirgin ruwan yaƙin Amurka ya harbo wani jirgin yaƙi mara matuƙi da makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi na Yaman suka harba, in ji rundunar sojin Amurka.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta fitar ta ce, jirgin yaƙin USS Mason [DDG 87] ya harbo wani makami mai linzami guda ɗaya a Kudancin Tekun Maliya da Houthis suka harba.

CENTCOM ta ƙara da cewa, babu wata ɓarna da aka samu ko ɗaya daga cikin jiragen ruwa 18 da ke yankin, sannan babu wanda ya samu raunuka, inda ya ƙara da cewa shi ne karo na 22 na yunƙurin kai hari kan jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa da Houthis suka yi tun tsakiyar watan Oktoba.

#