Yakin da Isra'ila take yi kan al'ummar Gaza da aka yi wa ƙawanya ya shiga rana ta 203, inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 34,305 - kashi 70% jarirai ne da yara da mata - tare da raunata sama da mutum 77,293.
0825 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama Falasɗinawa 7 a samamen da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (Wafa) ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kama Falasɗinawa bakwai, cikinsu har da wata mace, a samamen da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan ranar Juma'a da sanyin safiya.
A yankin Ramallah, wasu sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin ƴan gudun hijira na Al-Jalazon, inda suka tsare Falasɗinawa uku, ciki har da wata mace mai shekara 33 mai suna Jehad Nakhla.
A lardin Jenin, dakarun Isra'ila sun shiga garin Qabatiya sannan suka kama Falasɗinawa biyu bayan sun yi bincike a cikin gidansu.
Wasu sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin ƴan gudun hijira na Balata da ke arewacin birnin Nablus da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, inda suka tsare wani Bafalasɗine.
2330 GMT — Ana zargin Isra'ila da sace ɓsassan jiki daga gawawwakin da aka gano a kabarin bai-ɗaya a Gaza
Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatan jinya da masu aikin ceto sun tayar da shakku kan satar sassan jikin da sojojin Isra'ila ke yi bayan gano gawarwakin fararen hula daga kaburburan bai-ɗaya.
Likitoci da masu ceto sun gano akalla gawarwakin muumm 392 a Asibitin Nasser da ke Khan Younis. Kimanin 165 daga cikinsu har yanzu ba a san ko su waye ba bayan an gano gawarwakinsu sun lalace inda aka cire wasu sassan jikinsu.
Likitoci sun bayyana cewa an samu wasu gawarwaki tare da yanke cikinsu da dinke su ta wani salo da ya sha bamban da dabarun rufe raunuka da aka saba yi a Gaza, lamarin da ya sanya ake zargin satar gaɓoɓi, yayin da aka ga gawar wata ƙaramar yarinya sanye da rigar tiyata an cire wasu sassan jikinta, lamarin da ke nuni da cewa an binne ta tun tana raye.
Rahoton ya ce, an gano gawarwakin mutane da dama a lullube da baƙƙe da shuɗayen ledoji - irin waɗanda ake amfani da su wajen ƙara yawan zafin jiki - da suka sha bamban da launin likkafanin da ake amfani da su a Gaza, lamarin da kuma ke nuni da cewa Isra'ila na son hanzarta ɓoye hujjoji.