Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0615 GMT — Dakarun Isra’ila sun afka cikin asibitin Al Shifa
Dakarun Isra'ila sun afka asibitin Al Shifa na Gaza a ranar Laraba da safe bayan sun shafe lokaci suna harba rokoki da makamai a asibitin
Shugaban asibitin Dakta Ahmad Mikhallalati wanda shi ne shugaban asibitin mafi girma a Gaza a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa a yanzu haka tankokin yaki Isra’ila da buldoza na cikin harabar asibitin.
Tun da farko a ranar Laraba da safe, sojojin Isra’ila sun tabbatar da cewa sun kaddamar da hari kan Asibitin Al-Shifa.
0550 GMT — Dakarun Houthi sun ce sun kai hari kan Isra'ila a ranar Talata
Kungiyar Houthi a ranar Talata da dare ta bayyana cewa ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra’ila.
“Sojojinmu sun harba makamai masu linzami a wurare daban-daban da Isra’ila ta mamaye a yankunan Falasdinu,” in ji mai magana da yawun kungiyar Yahya Saree.
Ya bayyana cewa daga cikin wuraren da asuka kai hari akwai wasu “muhimman wurare” da ke kudancin birnin Eilat.
Saree ya ce kungiyar ta Houthi ta lashi takobin kai hari kan duk wani jirgin ruwan Isra’ila a cikin Tekun Bahar Maliya ko duk wani wuri da za su iya kaiwa.
0304 GMT — 'Dole a kare asibitoci da marasa lafiya' : Fadar White House
Dole a kare asibitoci da majinyatan da ke cikinsu "dole ne a kiyaye su," a cewar Fadar White House a lokacin da aka tambaye ta game da harin da ƙawarta Isra'ila ta kai a babban asibitin Gaza na Al Shifa.
"Ba za mu yi magana a kan takamaiman aikin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da yi ba. Kamar yadda muka ce, ba ma goyon bayan harin sama da ake kai wa kan wani asibiti, kuma ba ma son ganin musayar wuta a asibitin da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba suke, wadanda ba su da mataimaka.
"Mutane, marasa lafiya da ke ƙoƙarin samun kulawar jinya da suka cancanta a kula da su, amma suna samun kansu a cikin tashin hankali. Dole ne a kiyaye asibitoci da marasa lafiya, "in ji mai magana da yawun Kwamitin Tsaro na Fadar White House.
0104 GMT — Hamas ta zargi Biden yayin da Isra'ila ta afkawa asibitin Al Shifa na Gaza da tankunan yaki
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta ɗora alhakin kai farmakin da sojoji ƴan mamaya na Isra'ila suka kai a Asibitin Al Shifa, a kan Shugaba Biden" yayin da sashen ƴan ƙuna na asibitin ya ce tankunan Isra'ila na cikin ginin a yanzu haka.
Da sanyin safiyar yau Laraba Hamas ta ce sanarwar da hukumar leken asirin Amurka ta fitar, inda Amurka ta goyi bayan matakin da Isra'ila ta dauka na cewa mayakan Hamas na gudanar da ayyukansu a Asibitin Al Shifa, "wani ƙarin haske ne" kan kutsen da aka yi a asibitin.
"Amincewar Fadar White House da Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon kan labarin karya na Isra'ila, da ke ikirarin cewa Hamas na amfani da Asibitin Al Shifa don tsara kai hare-hare, alama ce da ke nuna cewa ƴan mamayar za su ci gaba da yi wa farare hula kisan kiyashi," in ji Hamas.