Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 175 tana yi a yankin Gaza da ta mamaye, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 32,552 sannan ta jikkata fiye da mutum 74,980 a yayin da Kotun Duniya ta umarce ta da ta daina jefa Gaza cikin bala'in yunwa.

Kai-tsaye: Amurka na so a yi bincike kan bidiyon da ya nuna sojojin Isra'ila suna binne mutane da ransu

0415 GMT — Amurka na so a yi bincike kan bidiyon da ya nuna sojojin Isra'ila suna binne mutane da ransu

Amurka ta ce ta yi matuƙar "damuwa" da ganin wani bidiyo wanda ya nuna dakarun Isra'ila sun harbi Falasɗinawa biyu da ba su ɗauke da makami sannan suka binne su da katafila, inda ta yi kira a gudanar da bincike.

A yayin da aka tambaye shi game da bidiyon, kakakin Ma'aikatar Tsaron Amurka ya shaida wa Anadolu cewa ba su tantance sahihancin bidiyon ba, yana mai ƙarawa da cewa za su yi gaggawar neman ƙarin bayani daga gwamnatin Isra'ila.

"Muna sa rai za a yi cikakken bincike game da wannan batu, idan kuma aka gano gaskiya nem a ɗauki mataki," in ji mai magana da yawun ma'aikatar tsaron ta Amurka.

"Kazalika, mun bayyana ƙarara cewa wajibi ne ga Isra'ila ta gudanar da bincike game da zarge-zargen da ake yi mata na keta dokokin yaƙi, sannan ta tabbatar da adalci da kuma ɗaukar matakai na hana sake aukuwar hakan," a cewarsa.

Wani bidiyo da sashen Larabci na gidan talbijin na Al Jazeera ya watsa ya nuna mutanen biyu suna tafiya a sarari a gaɓar tekun Gaza inda suka riƙa ɗaga fararen ƙyallaye da ke nuna zaman lafiya kafin sojojin Isra'ila su kashe su.

#