Asusun ba lamunin ya ce tallafin mai na dai-daya na da tsada, ya fi yawan taimaka wa masu hannu da shuni, kuma yana ta'azzara matsi kan tsarin kuɗi cikin ƙarin tsadar bashi.
Asusun ba da lamuni na IMF ya shawarci gwamnatin tarayyar Nijeirya kada ta dawo da tallafin man fetir gabaɗaya, tana mai ba da shawarar a tallafa wa gidaje masu rauni, irin tallafi da zai rage musu raɗaɗin tashin farashin makamashi.
Asusun ya ce ba da tallafin mai na bai-ɗaya na da tsada, inda a mafi yawan lokaci masu hannu da shuni suka fi amfana da shi, kuma yake ƙara matsin tsarin kudi a cikin ƙarin tsadar bashi.
Daraktan ɓangaren da ke kula da harkokin kudi a asusun IMF, Rodrigo Valdes ne ya bayyana wannan a lokacin wani jawabi ga manema labarai a taron shekara shekara na IMF da Bankin Duniya a Bangkok.
Kalamansa sun zo ne bayan wata tambaya da aka yi game da yadda asusun zai ba da shawara a bar farashi ya y tsada inda ƙarin kudin mai a Nijeriya zai iya ƙara farashin ababen hawa da ta’azzara tsadar rayuwa da zurfafa talauci, musamman yayin da gwamnatin ke fuskantar kiraye-kiraye na dawo da tallafin mai gabanin shekarar zaɓe.
“Kare mutane ba ɗaya ba ne da kare farashin mai,”in ji Valdés.
Ya ce tallafin mai ko kuma matakan da ke hana farashin sauyawa bisa girgizar makamashi ya sa ƙasashe sun rasa kashi 1 zuwa kashi 1.5 na tattalin arzikinsu a ma’aunin GDP a shekarar 2026.
Ya ce maimakon hakan ya kamata gwamnatin ta yi amfani da tsare-tsaren kare walwalar jama’a da kuma bayanai gidaje domin gano wadnada suke buƙatar taimako.
Kwannan nan ne gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi shelar ragin farashin man fetur na kwana 30 a gidajen mai na kamfanin man ƙasar NNPC a fadin ƙasar, inda za a ba da fifiko ga masu amfani da ababen hawa na kasuwa, domin rage raɗaɗin tashin farashin man fetur a ƙasar.

