A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Lahadi, ya ce “ɗimbin bashin ya sanya matsi sosai kan kamfanin kuma yana barazana ga ɗorewar shigo da fetur”.
Kamfanin mai na gwamnatin Nijeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya amince cewa "masu shigo da fetur" suna binsa "dimbin bashi", wanda ya ce yana barazana ga ɗorewar tsarinsa na shigo da fetur ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Lahadi, ya ce “ɗimbin bashin ya sanya matsi sosai kan kamfanin kuma yana barazana ga ɗorewar shigo da fetur”.
“Kamar yadda Dokokin Kamfanonin Man Fetru suka tanada, NNPCL zai ci gaba da sadaukawa a kan aikinsa na kasancewa madogara ta ƙarshe game da shigo da fetur, domin tabbatar da yalwar makamashi," in ji sanarwar.
Muna ci gaba da sabunta wannan labarin...