A rana ta 328 da Isra’ila ta fara yaki a Gaza, ta kashe a kalla Falasdinawa 40,602 – mafi yawan su mata da yara – tare da jikkata sama da 93,855, inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na karkashin buraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam.

Hamas ta yi maraba da tsagaita wuta da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsara don jinƙai a yakin Gaza

1725 GMT — Hamas ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ta tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza don aiwatar da allurar rigakafin polio.

Jami'in Hamas Basem Naim ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ƙungiyar a shirye take ta ba da haɗin kai ga kungiyoyin ƙasa-da-ƙasa.

Goyon bayan Amurka ga Isra’ila ne ke hana tsagaita wuta a Gaza — Hamas

Shugaban 'yan Dimokuraɗiyya Yair Golan ya yi kira ga shugabannin jam'iyyun adawa a Isra'ila su gudanar da taron gaggawa domin kawar da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.

Wani saƙon murya da Golan ya wallafa a shafinsa na X ya ce, "A yau, na tuntuɓi dukkan abokaina a jam'iyyun adawa inda na gaya musu saƙona ƙarara cewa ya kamata mu kama hanya iri ɗaya."

Ya ƙara da cewa, "Isra'ila tana cikin mawuyacin hali kuma tana durƙushewa a fannin siyasa da fannin tattalin arziki da mu'amala da kundin tsarin mulki.

"Komai yana wargajewa a idanunmu. Dole mu yi aiki tare kuma cikin tsanaki tare da jajircewa."

Golan ya wallafa saƙon da ya tura wa shugabannin jam'iyyun adawa, da ke cewa: "Muna tsaka da yaƙi, inda aka kwashe kwana 328 ana garkuwa da mutanenmu, kana an raba dubban mutane da gidajensu, sannan tattalin arzikinmu yana durƙushewa, kuma sojojinmu sun kwashe tsawon lokaci suna yaƙi ba tare da samu mafita ba.

"Rashin amincewa da gwamnati da kuma matakan da take yin gaban kanta wajen ɗaukarsu bisa muradunta na siyasa su suka tilasta mana yin wannan yunƙuri."

Da yake yin martani ga saƙon Golan, shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i."

Shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i." / Hoto: Reuters
#