EFCC ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn.
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon-ƙasa (EFCC) ta ce ta kama tsohon Ministan Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundaha.
Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ne ya tabbatar da hakan ranar Talata a ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja.
Ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za su gurfanar da Sirika tare da ɗan'uwansa Abubakar a gaban kotu kan zargin almundahar N8.06 bn.
Rahotanni sun ce zargin da ake yi wa tsohon ministan yana da alaka da yadda ya tafiyar da batun ƙaddamar da jirgin saman Nijeriya, wato Nigeria Air.