Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kuɗin da aka biya daga wani asusun tallafin cirani da gudun hijira zai kasance karo na farko na tura kuɗi tsakanin gwamnati zuwa gwamnati daga asusun, in ji sanatan.
Gwamnatin Shugaba Trump ta tura dala miliyan 7.5 ga gwamnatin ƙasar Equatorial Guinea yayin da take neman ta tasa ƙeyar mutane zuwa ƙasar ta Yammacin Afirka da kuma matsawa kusa da shugabanninta da Amurka ta ƙaƙaba wa takunkumi, in ji wata babbar sanata a kwamitin harkokin wajen na majalisar dattawan ƙasar.
Sanata Jeanne Shaheen, ta bayyana a wata wasiƙar da ta tura ranar Litinin ga Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio cewa “wannan tura kuɗin wanda ya saɓa wa al’ada sosai ya janyo wata babbar damuwa game da amfani da dalolin Amurkawa masu biyan haraji."
Shaheen ta bayyana a wasiƙarta cewa biyan dala miliyan 7.5 ya fita daban domin zai “zarce sosai adadin tallafin da Amurka ta bayar cikin shekaru takwas da suka wuce” ga ƙasar.
Kuɗin, wanda aka biya daga asusun tallafi na cirani da gudun hijira, zai kasance karo na farko da aka tura kuɗi daga gwamnati zuwa gwamnati daga asusun, wanda majalisar dokokin ta assasa a matsayin martani ga matsalar jinƙai.
Ta yi tambaya kan ko biyan kuɗi hanya ce da ta dace a kashe kuɗin Amurka a kai.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ƙi tsokaci game da cikakken bayani kan tattaunawa ta diflomasiyyar, amma ta ce, “ƙaddamar da manufofin shige da fice da gwamnatin Amurka abu ne da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fi bai wa fifiko.
“Kamar yadda Sakatare Rubio ya faɗa, babu ja da baya a jajircewarmu na kawo ƙarshen shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba da kuma shigowar mutane da yawa tare da ƙarfafa tsaron kan iyakokin Amurka.”
Gwamnatin Trump, yayin da take ƙoƙarin ƙara yawan mutanen da take kora daga ƙasar ta nemi ƙulla yarjejeniyoyi da wasu ƙasashe domin su kar karɓi ‘yan ciranin da ba ‘yan ƙasarsu ba ne.
Ƙungiyoyin ‘yan gwagwarmaya sun soki manufa “ta ƙasa daban” a matsayin wata dabara mara tunani.
Nijeriya dai ta ƙi amincewa da yarjejeniyar inda kwanakin baya Ministan Hrkokin Wajen ƙasar Yusuf Tuggar ya ce Nijeriya ta ƙi ne saboda matsalolinta sun ishe ta ba sai ta karɓi masu laifuka ‘yan wasu ƙasashe daga Amurka ba.
Baya ga tasa ƙeyar mutanen, Amurka na ƙoƙarin rage tasirin China a Equatorial Guinea da kuma bunƙasa harkar man Amurka a ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment