Duk da ƙarin matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati sakamakon tallafin fetur, gwamnatin ta ce ba za ta ɗauki shawarar da Majalisar Tuntuɓa kan Farfaɗo da Ƙasa (CCR), wadda ke aiki a matsayin majalisar dokokin riƙon ƙwarya ta ƙasar ta bayar ba.

Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar karin farashin man fetur a ƙasar

Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa ba za ta ƙara farashin man fetur ba, duk da ƙarancinsa da ake fama da shi da kuma ƙarin matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati sakamakon tallafin man fetur.

Gwamnatin ta sanar da matakin ne bayan taron Majalisar Ministoci da aka gudanar a ranar Jumma’a, 9 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Abdourahamane Tiani. Ta yi watsi da shawarar Majalisar Tuntuɓa kan Farfaɗo da Ƙasa (CCR), wadda ke aiki a matsayin majalisar dokokin riƙon ƙwarya ta ƙasar, na ƙara farashin man fetur da wani adadi da ta kira “mai ma’ana”, domin rage nauyin kuɗin tallafin da gwamnati ke biya.

Shugaba Tiani ya sake jaddada cewa farashin litar man fetur zai ci gaba da kasancewa CFA 499, yayin da litar dizal za ta ci gaba da kasancewa CFA 618. Ya kuma nanata cewa albarkatun ƙasar dole ne su kasance masu amfani ga al’ummar Nijar.

Gwamnatin ta danganta matsalolin samar da man fetur da ƙalubalen tsarin aiki da shugabanci a matakai daban-daban na samarwa, sufuri da rarraba man fetur. Ta kuma ce hanyoyin sayar da man da ba na hukuma ba da kuma zamba suna ƙara ta’azzara ƙarancinsa da tashin farashinsa.

Domin shawo kan matsalar, hukumomin ƙasar sun sanar da kafa wani kwamitin aiki da zai gano matsalolin da ke kawo cikas ga samar da man fetur da rarraba shi, tare da gabatar da shawarwarin magance su. Haka kuma, an umarci hukumomin sa ido da su gudanar da bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a harkokin zamba da aka tsara a ɓangaren man fetur.

Ƙarancin man ya jawo dogayen layuka a gidajen mai a biranen Maradi, Zinder da Agadez, yayin da ƙarancin wadatarsa ya ƙara jawo yawaitar sayar da man a kasuwar bayan fage.

Ministan Man Fetur, Hamani Tinni, ya shaida wa mambobin CCR cewa giɓin samar da man fetur ya kai lita miliyan 196.62 a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2026, adadin da ya zarce lita miliyan 159.74 da aka samu a dukkan shekarar 2025.

Gwamnatin ta ce tana nan daram kan ƙudurinta na tabbatar da samar da man fetur a kai a kai, ba tare da ƙara tsadar rayuwa ga al’umma ba.

 

 

#