A 'yan makonnin nan, kasar Gambia ta fuskanci zanga-zanga sakamakon katsewar wutar lantarki da ruwa.
Kasar Gambia ta karɓi sabbin injinan samar da wuta guda biyu masu ƙarfin megawatt 21 domin magance matsalar ƙarancin wutar lantarki da ta addabi ƙasar.
Tun daga watan Yuni, Gambia ke fama da matsalar katsewar wuta ta tsawon lokaci, lamarin da ya tsananta a makonnin baya bayan nan, wanda ya zo a daidai lokacin da ake tsananin zafi, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar.
Injinan, waɗanda kowannensu ke da ƙarfin megawatt 10.5, sun isa tashar jiragen ruwa ta babban birnin ƙasar, Banjul, a ranar Litinin daga ƙasar China inda aka sayo su.
Shirin samar da mafita ta dindindin
"Samar da waɗannan injina wani ɓangare ne na matakan magance ƙalubalen wutar lantarki da ake fuskanta. Gwamnati na son amfani da su a matsayin shirin da take yi na matsakaici da dogon zango don magance matsalar wutar lantarki ta dindindin," in ji Mataimakin Shugaban Kasa Muhammed Jallow.
Shugaban kamfanin samar da wuta da ruwa na ƙasar (National Water and Electricity Corporation) ya bayyana cewa za a dasa injinan wutar tare da soma amfani da su kafin ƙarshen wannan watan.
"Ba a taɓa amfani da waɗannan injina ba, abin da kawai ake buƙata shi ne a sanya su a wurin da za su yi aiki," in ji Gallo Saidy.
