Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Ankara na aiki sosai don tabbatar da cewa kasashen duniya ba su yi biris da keta hakkokin ɗan'adam da laifukan yaƙi da Isra'ila ke aikatawa ba.

Erdogan ya buƙaci ƙasashen duniya da su mayar da hankali kan laifukan yaƙi da Isra'ila ke aikatawa a Gaza

Shugaban Kasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan ya bayyana irin kokarin da kasarsa ke yi na janyo hankalin kasashen duniya ga abu marar kyau da Isra'ila ke yi tsawon watanni a Gaza.

"Muna yin kokari sosai wajen tabbatar da cewa kasashen duniya ba su yi biris da keta hakkokin dan'adam da laifukan yaki da Isra'ila ke aikatawa ba," in ji Erdogan a ranar Juma'a a sakon bidiyo da ya aike ga Babban Taron Matasan Kasashe Mambobin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai.

Da yake bayyana muhimmancin ayyukan diflomasiyya na hadin gwiwa a tsakanin kasashen Musulmai don mayar da martani ga zaluncin Isra'ila a Gaza, Erdogan ya ambaci ayyukan diflomasiyyar da ake yi don karfafa martanin hadin kai da goyon baya.

'Falasdinu Mai Cin Gashin Kai'

Haka zalika, Erdogan ya sake jaddada yunkurin Turkiyya na bayar da goyon baya don tabbatuwar 'yantacciyar kasar Falasdinu da dukkan duniya ta amince da ita.

Ya ce "Za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai an samar da kasar Falasdinu mai 'yanci tare da kare iyakokin da da aka fitar a 1967, kuma Jerusalem ya zama babban birnin kasar."

A ranar 7 ga Oktoban 2023 ne Isra'ila ta fara kai hare-hare Gaza bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai musu wani hari.

Ya zuwa yanzu an kashe Falasdinawa 27,585 inda aka jikkata wasu 66,978. An kuma kashe 'yan Isra'ila 1,200.

Hare-haren Isra'ila ta raba kaso 85 na falasdinawa da matsugunansu, inda ake ta fama da rashin abinci da ruwan sha mai tsafta da magunguna.

Haka kuma an lalata kaso 60 na gine-ginen yankin Gaza, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

A wani hukunci da aka yi a watan da ya gabata a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, an fada wa Isra'ila ta dakatar da cin zarafin da take yi a Gaza, amma masu sanya idanu na kasa da kasa na cewa ta ki aiki da wannan hukunci.

#