Sport
Dollar
40,7874
0.01 %Euro
47,8899
0.17 %Gram Gold
4.405,5900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, hukumar EFCC ta ce ta ƙwace motoci 18 da wayoyi a hannun mutanen da ake zargi da damfarar.
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, EFCC, ta yi ƙarin haske kan samamen da ta kai Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke birnin Abeokuta a Jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.
Jaridun Nijeriya dai sun ambato hukumar gudanarwa ta OOPL tana ƙorafi game da abin da ta kira samamen tashin hankali da jami’ai fiye da 50 ɗauke da bindigogi suka kai Ɗakin Karatun da misalin ƙarfe biyu na dare.
Jaridun sun ambato sanarwar hukumar gudanarwar tana cewa jami’an EFCC sun kutsa ɗakin karatun suna “harbi, da barazanar kashe mutane tare da sanya fargaba ga baƙi da mazauna wurin.”
Hukumar gudanarwar OOPL ta ce jami’an EFCC sun yi dirar mikiya kan wasu mutane da ke biki a cikin otal ɗin da ke ginin ɗakin karatun cikin dare ba tare da gabatar da takardar sammaci ba.
Duk da cewa ba ta ambaci sunan ɗakin karatun na OOPL ba, hukumar EFCC ta tabbtar da cewa ta kai samamen a wani otel a birnin Abeokuta inda ta kama waɗanda ake zargi da damfarar intanet da aka fi sani da ‘yan Yahoo guda 93.
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar EFCC ta ce ta ƙwace motoci 18 da wayoyi daga hannun mutanen da ake zargi da damfarar.
Comments
No comments Yet
Comment