Dollar

40,7826

0.01 %

Euro

47,9020

0.18 %

Gram Gold

4.406,0600

0.14 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rahotanni sun ce Aminu Waziri Tambuwal ya isa hedkwatar EFCC ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Litinin.

Abin da ya sa EFCC ta kama tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal

Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa ta tsare tsohon gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal bisa zargin saɓa dokokin kuɗi.

Jaridun ƙasar sun ambato majiyoyi daga EFCC suna cewa an riƙe tsohon gwamnan a hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Litinin kan zargin cire naira biliyan 189 ba bisa ƙa’ida ba.

Kazalika wasu jaridun ƙasar sun ruwaito cewar hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan wanda ya taɓa zama shugaban majalisar wakilan ƙasar ne kan yadda ya cire kuɗaɗen daga banki abin da ya saɓa wa dokar haramta sama-da-faɗi da kuɗi ta 2022.

Sai dai Jam’iyyar PDP reshen Jihar Sokoto, a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ta ce kama tsohon gwamnan Jihar na cike da siyasa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Jam'iyyar PDP na Jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya ce kama Tambuwal wani yunƙuri ne na rufe bakin jam'iyyun adawa da tsorata su a ƙasar.

Sai dai wasu rahotanni sun ambato majiyoyi daga hukumar na cewa gayyatar Tambuwal kawai hukumar ta yi, ba kama shi ba ne.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#