Ƙasashen Yammacin Afirka a yayin taron da suka gudanar a Abuja sun buƙaci ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar su sake nazari game da ficewarsu daga ƙungiyar inda suka ƙara musu wa'adin wata shida domin su je su sake tunani.

ECOWAS ta ba Burkina Faso, Mali da Nijar wata shida su sake nazari kan fitarsu daga ƙungiyar

Ƙasashen Yammacin Afirka a ranar Lahadi sun bai wa ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji wata shida su sake nazari kafin ficewarsu daga ƙungiyar ECOWAS.

Wannan matakin na ECOWAS na zuwa ne bayan ƙasashen uku waɗanda suka kafa ƙungiyar Sahel Alliance sun jaddada cewa "ba za su koma ƙungiyar ta ECOWAS ba", amma za su amince a riƙa shige da fice a tsakanin ƙasashen ba tare da biza ba.

Ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da zama ‘yar ‘amshin-shata ga Faransa, wadda ita ce ta yi musu mulkin mallaka, amma a yanzu suka raba gari da ita.

Ficewar ƙasashen uku daga ECOWAS zai yi tasiri matuƙa kan kasuwanci da kuma zirga-zirgar jama'a da jigilar kayayyaki da kuma tsaro a yankin wanda ke fama da ta'addanci.

A ƙarƙashin dokar ECOWAS, ya kamata ficewarsu daga ƙungiyar ta zama ta fara aiki ne a watan Janairu mai zuwa, shekara guda bayan ƙasashen suka yi sanarwarsu ta farko ta ficewa daga ƙungiyar.

Sai dai bayan tattaunawar da aka gudanar da ƙungiyar ta gudanar a Abuja, ƙungiyar a cikin sanarwar da ta fitar ta ce ta saka tsakanin 29 ga Janairun 2025 zuwa 29 ga Yulin 2025 a matsayin wani wa'adi domin barin ƙofar ƙungiyar a buɗe ga ƙasashen uku ko da kuwa za su sake nazari kan ficewar tasu.

Haka kuma ƙungiyar ta ECOWAS a zaman da ta yi a ranar Lahadi 15 ga Disamba ta amince a kafa wata kotu ta musamman domin yin hukunci dangane da laifukan da aka aikata a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Gambia Yahya Jammeh.

#