Bankin Ci Gaban Afirka (AfDB) yana son ya tara dala biliyan 2.2 domin tallafa wa fannin noma a Nijeriya

Bankin Ci Gaban Afirka zai tara $2.2bn domin bunƙasa harkar noma a Nijeriya

Bankin Ci Gaban Afirka (AfDB) yana ƙoƙarin samar da dala biliyan 2.2 wajen haɓaka wuraren sarrafa amfanin gona a jihohi 28 na Nijeriya domin bunƙasa samar da abinci da ayyukan yi, in ji shugaban bankin Akinwumi Adesina ranar Talata.

Adesina ya faɗi a hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da mataki na farko na shirin da zai mayar da hankali kan jihohi biyar a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar. Wannan matakin ana yin sa ne da kuɗi sama da dala miliyan 500 da aka yi shelarsa a shekarar 2022.

Bankin na AfDB  ya ce za a gabatar da kuɗaɗen da ake buƙata domin ƙaddamar da mataki na biyu na shirin ga kwamitin gudanarwa na AfDB nan ba da jimawa ba domin samun amicewarsa.

"Zan so in bayyana cewa mun samu mun nemo jarin dala biliyan $2.2 domin tallafa wa mataki na biyu na shirin a fadin Nijeriya," in ji shugaban bankin a lokacin bikin a Kaduna.

Adesina ya ce baya ga AfDB, bankin raya tattalin arziƙi na Larabawa da kuma African Import and Export Bank mai inganta cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka da Caribbean da kamfanin hadadar kuɗi ta intanet mai suna Sahara Farms na cikin waɗanda za su taimaka wajen tara dala biliyan $2.2 ɗin.

Cibiyoyin sarrafa amfanin gonan dai an yi su ne da zummar samar da ababen sarrafa amfanin gona kusa da manoma, lamarin da zai rage asarar amfanin gona bayan girbi da tare da ƙarfafa hada-hada daga gona zuwa kasuwa.

A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta kashe dala biliyan $4.7 wajen shigo da abinci, kuma yadda AfDB ya bayyana, wannan wani yanayi ne da hukumomi ke ƙoƙarin sauyawa ta hanyar ƙara saka kuɗaɗe a fannin noma.

#