Sport
Dollar
41,2910
0.2 %Euro
48,4340
0.61 %Gram Gold
4.758,6800
1.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A shekarar 2023 ne aka zaɓi Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a matsayin shugaba da mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, sai da an yi ta raɗe-raɗin cewa Tinubu zai ajiye Shettima a zaɓen 2027.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yaba wa Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima a wani saƙo na bikin cikarsa shekara 59 da haihuwa, inda ya bayyana shi matsayin “abokin aiki” mai aminci wanda mutum zai iya yarda da shi a ƙoƙarin gina ƙasa mai wadata.
Ya ce sadaukarwar da Shettima yake yi wajen ganin an samu ci-gaba a Nijeriya ta tabbatar masa cewa bai yi kuskure ba wajen ɗaukarsa a matsayin mataimakinsa.
Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban ƙasar ya fitar kuma kakakinsa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X.
“A yau, 2 ga watan Satumba shekarar 2025, ta ba ni wata damar taya ka murna, ɗan’uwana abokin aikina kuma mataimakin shugaban ƙasa yayin da ranar haihuwarka ta zagayo,” in ji saƙon na Tinubu.
Ya yaba da jarumta da juriyar Shettima tun lokacin da ya haɗa kai da shi a kan hanyar sake wa ƙasar fasali.
“Tun da muka fara wannan tafiya, wadda hangen nesa na gina ƙasa mai wadata ya haɗa mu, jarumtarka da sanin ya kamata, da jajircewa da azama da yarda da girman Nijeriya bai taɓa kasancewa cikin shakka ba.
Comments
No comments Yet
Comment