Ministan wajen Turkiyya da takwaransa na Sifaniya sun tattauna a kan yaƙin Isra'ila a Gaza, da samar da dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakya da alaƙar Turkiyya da Tarayyar Turai a yayin da suka yi taron manema labarai na haɗin-gwiwa a Ankara.
Bai kamata a ƙyale buƙatar shigar Turkiyya cikin Tarayyar Turai a hannun "wasu tsirarun ƙasashe masu manufa ta siyasa ba," in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.
"Ina so na jaddada cewa bai dace a bar buƙatar Turkiyya ta shiga cikin Tarayyar Turai a hannu wasu tsirarun ƙasashe masu manufa ta siyasa ba," kamar yadda Fidan ya bayyana ranar Laraba a wani taron manema labarai na haɗin-gwiwa da takwaransa na Sifaniya Jose Manuel Albares da suka gudanar a Ankara.
His remarks came after a meeting held by the two ministers in Ankara.
Fidan ya ce tun da farko Sifaniya na cikin ƙasashen da suka yi tsayin-daka wurin goyon bayan Turkiyya domin ta shiga Tarayyar Turai, yana mai jaddada cewa shigar ƙasarsu cikin Tarayyar Turai wani abu ne mai muhmmanci ga gwamnatin Ankara.
Haɗin-kai don samar da tsaro a Bahar Rum
Kazalika ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce ƙasarsa da Sifaniya su ne ƙasashe biyu mafi muhimmanci a yankin Bahar Rum, wanda ke fuskantar ƙalubale da suka haɗa da ta'addanci da sauyin yanayi da ƙaura da sauransu.
”Turkiyya da Sifaniya, waɗanda suke gabashi da yammacin Bahar Rum, suna ganin tasirin waɗannan ƙalubale ƙarara. A matsayinmu na ƙasashe biyu da suka kwashe shekaru suna yaƙi da ta'addanci, muna ɗaukar batun haɗin-kai domin bunƙasa tsaro da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.
Haka kuma Fidan ya ce za a yi taro na takwas game da dangantakar Gwamnatin Turkiyya da ta sifaniya a watan Yuni.