Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa suna fuskantar irin wannan zargi.
Ofishin mai shigar da ƙara na Sudan ya zargi tsohon firaiministan ƙasar Abdalla Hamdok da laifin "tunzura" mutane domin su "yaƙi ƙasar" da kuma wasu laifuka da ka iya jawowa a yanke wa mutum hukuncin kisa, a cewar gidan talbijin na ƙasar
Ofishin mai shigar da karar yana biyayya ga shugaban mulkin soji Janar Abdel Fattah al Burhan, wanda tun watan Afrilun 2023 dakarunsa suke gwabza yaƙi da na mataimakinsa kuma shugaban dakarun sa-kai na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo.
Mutane goma sha biyar, ciki har da ƴan jarida da ƴan siyasa, waɗanda su ma suke zaune a ƙasashen waje, suna fuskantar irin wannan zargi na "keta kundin tsarin mulki".
Hamdok, wanda shi ne ɗan siyasa farar-hula mafi shahara a Sudan, ya rike muƙamin firaiministan ƙasar bayan tumɓuke gwamnatin Omar al Bashir.