Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ruwaito cewa an yi bikin miƙa ayyukan ne a wani taro da manyan jami’an gwamnati da wakilan kamfanonin ‘yan kwangila suka halarta a jihar.

An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina ajujuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar

Gwamnan jihar Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane, ya miƙa ayyukan gina makarantu 357 ga ‘yan kwangila a wani ɓangare na shirin inganta koyarwa a cibiyoyin ilimi, da ake ce wa Niger LIRE.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ANP ya ruwaito cewa an yi bikin miƙa ayyukan ne a wani taro da manyan jami’an gwamnati da wakilan kamfanonin ‘yan kwangila suka halarta a jihar a ƙarshen makon jiya.

Gwamnan ya ce miƙa wuraren ayyukan ga ‘yan kwangilar wani muhimmin mataki ne wajen inganta koyarwa a makarantun Nijar da kuma aiwatar da burin gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Abdourahamane Tiani na samar wa makarantun Nijar gine-gine na zamani da suka dace da ci-gaba.

Kanal-Manjo Bana Alhassane ya tuna wa kamfanoni da aka zaɓa muhimmancin aikin da aka ba su amanar yi, yana mai cewa hakan ya nuna yadda aka yarda da ƙwarewarsu.

Gwamnan ya ce ƙa’idoji uku da suka haɗa da ingancin aiki babu ƙaƙƙautawa da biyayya ga wa’adin aiki da kuma kare lafiyar ma’aikata su ne muhimman ƙa’idojin da za su tafiyar da ayyukan a duk wuraren da za a yi su.

Ya kuma ce matakai daban-daban na hukumomin da jami’an gwamnati za su tabbatar da sa ido na dindindin kan ayyukan domin tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin ayyukan yadda ya kamata.

Daga farko, jagoran shirin Niger LIRE, Djillou Idrissa, ya ce ayyukan da ake yi a ƙarƙashin sa idon Ma’aikatar Ilimi Ta Ƙasa da Ƙuma Ci-Gaban Harshe, an tsara su ne ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2020 da kuɗi na farko da ya kai dalar Amurka miliyan 140.

"An ƙara dala miliyan 230 ga shirin ne ranar 11 ga watan Oktoba na shekarar 2024, lamarin da ya mayar da kasafin kuɗin aikin zuwa dala miliyan 370," kamar yadda ANP ya ambato shi yana cewa.

Ya ce an riga an yi wasu ayyuka a jihar kan kuɗi na farko da aka fara bayarwa, ciki har da gyara makarantar koyar da malaman Firamare na Dosso da samar da komfutoci 213 ga hukumar ilimi ta yanki da makarantar koyar da malaman ta Dosso da kuma ababen haɗa na’urar samar da intanet ta Starlink 60 don sa ido kan makarantun firamare da sakandare.

Djillou Idrissa ya ce ƙarin kuɗin zai mayar da hankali ne kan gina ajujuwa da gine-gine masu alaƙa ciki har da ɗakunan gwaje-gwaje ga ƙanana da manyan makarantun sakandare.

#