Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun fi yara 100, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun sace gomman ɗalibai na wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a yau Alhamis.
Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun fi yara 100, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu.
TRT Afirka Hausa ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumomi na gwamnatin jihar da na jam'ian tsaro, amma ba a same su ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa waɗanda suka shaida lamarin sun ce abin ya faru ne a lokacin da yaran suke halartar taro na asambili, kana daga bisani ƴan bindigan su kora ɗaliban da suka sace ɗin cikin daji.
Ƴan bindiga da ke yawan kai hare-hare sun sha satar ɗalaibai a wasu jihohin arewacin Nijeriya, lamarin da yake yin mummunan tasiri a kan fannin ilimi a ƙasar.