Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa, ya kuma yi kira ga Washington da ta ci gaba da tallafa wa hukumar ko ma ta ƙara tallafin.

Amurka ta yaba wa NDLEA kan gano wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi masu alaƙa da ƙungiyoyin Mexico

Amurka ta yaba wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) bisa rusa dakunan sarrafa ƙwayar methamphetamine guda huɗu masu girman masana’antu da ke da alaƙa da ’yan ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi na Mexico.

Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa, ya kuma yi kira ga Washington da ta ci gaba da tallafa wa hukumar ko ma ta ƙara tallafin.

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da yaƙi da miyagun ƙwayoyi da harkokin tabbatar da doka a Afirka da Gabas ta Tsakiya, Michael Gonzales, ya yaba wa ayyukan hukumar da suka dogara da bayanan sirri yayin ziyarar da ya kai hedikwatar NDLEA da ke Abuja ranar Talata.

Marwa ya ce an gano dakunan sarrafa ƙwayoyin a jihohin Ogun, Oyo, Enugu da Ebonyi. Ya yi gargaɗin cewa ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasashen waje na ƙoƙarin mayar da Nijeriya cibiyar ƙera methamphetamine da fitar da ita zuwa ƙasashen waje.

An gano mafi girman masana’antar a Ijebu East, Jihar Ogun, inda aka kama ƙwararrun sarrafa methamphetamine ’yan Mexico uku tare da abokan aikinsu ’yan Nijeriya. An kuma kwato haramtattun abubuwa da darajarsu ta haura dala miliyan 360.

Marwa ya yi gargaɗin cewa fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙara haɗuwa da fataucin makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma samar da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci, musamman a yankin Sahel da tafkin Chadi. Ya ce hakan na buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe.

Ya bayyana cewa tallafin Amurka ya ƙarfafa ƙarfin NDLEA wajen binciken sinadarai, horar da jami’ai da binciken laifukan kuɗi.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, hukumar ta kama masu laifin miyagun ƙwayoyi 96,157, ta ƙwace sama da kilogiram miliyan 15.8 na haramtattun ƙwayoyi, sannan ta samu hukuncin kotu kan mutane 16,691.

Marwa ya buƙaci Washington ta ci gaba da tallafa wa hukumar ko ma ta ƙara tallafin, yana mai gargaɗin cewa rage tallafin na iya ba ƙungiyoyin masu aikata laifuka da na ta’addanci damar faɗaɗa ayyukansu.

#