Farfesa Amupitan ya ce hukumar INEC, a ƙarƙashin shugabancinsa, ta bi jadawali da ƙa’idoji sahu da ƙafa a cikin shirye-shiryen da take yi.
Shugaban Hukumar Zaɓen Nijeriya (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da sahihan zaɓuka a shekarar 2027.
Amupitan ya bayyana haka ne ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabi a taron “Tantance shiri don zaɓukan 2027” ga ma’aikatan hukumar a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Nijeriya.
Ya ce hukumar, a ƙarƙashin jagorancinsa, ta bi jadawali da ƙa’idojin zaɓe sahu da ƙafa a cikin shirye-shiryen da take yi.
“Muna kan hanya kuma muna aiwatar da yawancin ƙa’idojin zaɓe. Mun samu kayayyakinmu mara muhimmanci sosai kuma mun rarraba su yayin da muke ci gaba da ba da kwangilar kayayyaki masu muhimmanci.”
“Hukumar tana samun ƙarin motoci na sufuri domin jigilar ma’aikata da kayayyaki ba tare da matsala ba.
“An fara horaswa da sake horaswa na mutane da yawa musamman kan sabbin ƙa’idoji da dokoki da aka shigar cikin dokar zaɓe da aka gyara,” in ji shi.
Ya ce an inganta fasahar sadarwar hukumar tare da ƙarfafa tsaronta.
Shugaban INEC ya ce hukumar ta kafa wasu jerin kwamitoci da suka ƙunshi hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin ba da gudunmawa ta musamman don tabbatar da nasarar gudanar da zaɓukan.
Daga farko dai, shugaban INEC a jihar Enugu, Dr Chukwuemeka Chukwu, ya ce jihar Enugu ta ƙunshi ƙananan hukumomi 17 da wuraren rajista 260 da kuma mazaɓu 4,145.
“Tafiyar da lamuran zaɓe a faɗin irin wannan wuri mai yawa na buƙatar isassun ma’aika da kayayyakin sufuri da fasaha da ababen more rayuwa da tsarin tsaro da ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a yankunan karkara.”
“Tarihin hukumar ya nuna cewa ko wane ɓangare na zaɓe na da alaƙa sauran ɓangarorin.
“Saboda haka dole shirye-shoiryenmu a matakin ƙananan hukumomi da yankunan rajista da mazaɓu a yi su yadda ya dace da shirye-shiryenmu na yanki da na ƙasa.
“Dole mu mu ci gaba da ƙarfafa tsare-tsarenmu da inganta matakan aikinmu da kuma tabbatar da cewa ko wane jami’i ya gane nauyin da ya ratayu a kansa wajen nasarar gudanar da zaɓukan 2027,” in ji Chukwu.
Wakilai daga jihohi biyar na Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo, sun gabatar da jawabai game da shirin jihohinsu da ƙalubalen da suke fuskanta gabanin zaɓukan.

