Sport
Dollar
40,9411
0.09 %Euro
47,9607
0.44 %Gram Gold
4.383,8900
0.13 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tuni hukumar DSCA mai kula da tsaron Amurka tare da manufofin ƙasashen wajen ƙasar ta miƙa takardun shaidar da ake buƙata don sanar da Majalisar Dokokin Amurka game da yiwuwar sayar da makaman.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da yiwuwar sayar wa Nijeriya makamai da bamabamai da rokoki na kimanin dala miliyan 346 (kimanin naira biliyan N532), in ji ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon.
Tuni hukumar DSCA mai kula da tsaron Amurka tare da manufofin ƙasashen wajen ƙasar ta miƙa takardun shaidar da ake buƙata don sanar da Majalisar Dokokin Amurka game da yiwuwar sayar da makaman.
“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yanke hukuncin amincewa da yiwuwar sayar da makamai ga sojin ƙetare zuwa ga gwamnatin Nijeriya, in ji wata sanarwa.
Sanarwar ta ce makaman da kuɗinsu zai kai dala miliyan $346 sun haɗa da bamabamai da rokoki waɗanda ke kai hari bisa saiti.
Comments
No comments Yet
Comment