Sport
Dollar
38,7786
0.39 %Euro
43,8944
0.27 %Gram Gold
4.147,5900
1.06 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Biyo bayan wannan alkaluma dai, gwamnatin tarayya kasar ta sanar da sake daukar wasu matakan dakile fasa-kwaurin abinci da rashin tsaftar abinci a kasar.
Kimanin ‘yan Nijeriya 200,000 wadanda mafi yawa daga cikinsu yara ne ke rasa rayukansu a duk shekara sakamakon cututtuka masu nasaba da abinci.
Kazalika, kasar na yin hasarar kusan dala biliyan 3.6 duk shekara sakamakon rashin lafiya da ta shafi gurbataccen abinci, a cewar ministan kere-kere, da kimiyya da kuma fasaha, Uche Geoffrey Nnaji. Ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da littafin alkinta abinci na masu sana’ar abinci, da kasuwanci, da kuma sauran masu sayar da abinci a kan titi a Abuja, ranar Alhamis.
Biyo bayan wannan alkaluma dai, gwamnatin tarayya kasar ta sanar da sake daukar wasu matakan dakile fasa-kwaurin abinci da rashin tsaftar abinci a kasar.
Don magance cututtukan da abinci ke haifarwa, Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kimiyya da Fasaha ta Nijeriya (NiCFoST), sun ƙaddamar da Littafin Ayyukan Tsaro na Abinci a karon a Nijeriya don ƙarfafa tsarin abinci, da inganta rayuwa, da rage yawan rashin lafiya, da maido da amincin jama'a game da lafiyar abin da 'yan Nijeriya ke ci.
Uche Nnaji, wanda ya bayyana rashin tsaftataccen abinci a matsayin “annobar da ba ta da tushe”, ya jaddada bukatar magance kalubalen gaggawa da ke fuskantar matsalar abinci a fadin Nijeriya, musamman a bangaren da ba na yau da kullun ba.
Ya bayyana cewa, kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna cewa sama da mutane miliyan 600 ne ke fama da rashin lafiya a fadin duniya a duk shekara sakamakon gurbacewar abinci, inda Afirka ke da adadi mafi girma na yawan mutane.
Comments
No comments Yet
Comment