Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A wani rubutu Trump ya ce: “Na soke dukkan ganawar da zan yi da jami'an Iran har sai an daina kai wa masu zanga-zanga hari. Taimako na kan hanyarsa. MIGA!!!”

'Taimako yana zuwa' in ji Trump ga masu zanga-zanga a Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga masu zanga-zanga a Iran su ci gaba da yin zanga-zanga kuma su ƙwace hukumomi, yana cewa “tallafi na kan hanya” yayin da ya yi gargaɗin cewa jami'an Tehran za su ɗanɗana kuɗarsu.

A saƙon da ya wallafa a kafar Truth Social a ranar Talata, Trump ya ce: “’Iraniyawa masu kishin ƙasa, ku ci gaba da zanga-zanga, ku ƙwace iko da hukumominku!!! Ku adana sunayen masu kisan kai da masu cin zarafi. Za su ɗaɗana kuɗarsu.”

Ya ƙara da cewa ya soke dukkan ganawar da zai yi da jakadun Iran.

A wani rubutu Trump ya ce: “Na soke dukkan ganawar da zan yi da jami'an Iran har sai an daina kai wa masu zanga-zanga hari. Taimako na kan hanyarsa. MIGA!!!”

Trump yana amfani da gajeriyar kalma ta MIGA a matsayin kalaman da ya saba yi mai take 'Make America Great Again', wato “A sake mayar da Amurka ƙasaitacciya”, amma a wannan karon Iran yake nufi.

A ranar Litinin, Fadar White House ta ce shugaban Amurka "yana da sha'awa" wajen nazarin yiwuwar diflomasiyya da Iran.

Mai magana da yawun Fadar, Karoline Leavitt, ta ce Trump "bai jin tsoro" wajen aiwatar da barazanar amfani da karfin soja kan wuraren da suka shafi Iran idan jami'an tsaro sun kai wa masu zanga-zanga hari, amma ta ce abin da ya fi so shi ne bin hanyoyin diflomasiyya da Tehran.

Jami'an Iran sun zargi Amurka da Isra'ila da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin "masu tarzoma masu makamai", wadanda suka kai hari a wasu wuraren jama'a a fadin ƙasar.

Babu adadin waɗanda suka rasa rayukansu a hukumance, amma wata ƙungiyar kare hakkin bil'adama da ke Amurka ta ƙiyasta cewa adadin mamatan ya kai a kalla 646, ciki har da jami'an tsaro da masu zanga-zanga, yayin da fiye da 1,000 suka ji rauni.

Ƙungiyar ta kuma ruwaito cewa an tsare akalla mutum 10,721 masu zanga-zangar a wurare 585 a fadin ƙasar, ciki har da birane 186 a dukkan larduna 31.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#