Sabon ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee ya ceto ƙungiyar daga hannun Fulham bayan ya zura ƙwallon da ta ba su nasara a wasansu na farko na gasar Firimiya ta bana.
Sabon ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee ya ceto ƙungiyar daga hannun Fulham bayan ya ci ƙwallo a wasan da suka tashi da ci 1-0 a karawarsu ta farko ta gasar Firimiya ta bana.
Ɗan wasan ɗan ƙasar Netherlands ya zura ƙwallon ce a minti na 87 lokacin da Alejandro Garnacho ya miƙa masa ƙwallon a fafatawar da suka yi a filin wasa na Old Trafford ranar Juma'a da maraice.