Wasu hotuna da kafar yaɗa labaran gwamnati Fana Broadcasting Corporate ta wallafa a Facebook sun nuna ɗaruruwan mutane kusa da inda lamarin ya faru, sun yi buɗu-buɗu da jar ƙasa.

Zaftarewar ƙasa ta yi ajalin aƙalla mutum 55 a Ethiopia

Aƙalla mutum 55 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a wani yanki mai nisa a kudancin Habasha a ranar Litinin, kamar yadda hukumomi suka faɗa, suna masu gargaɗin cewa adadin waɗanda suka mutu zai iya haura haka.

“An gano gawawwaki fiye da 55 a zaizaiyar ƙasar,” kamar yadda wata sanarwa daga Sashen Watsa Labarai na yankin Gofa ya bayyana, yana ambato jagoran yankin Dagmawi Zerihun yana gargaɗin cewa, adadin waɗanda suka mutu ɗin zai iya ƙaruwa.

Zaizaiyar ƙasar ta faru ne da misalin karfe 10 na safe, bayan mamakon ruwan sama a yankin mai tsaunuka a yankin da ke Kudancin Ethiopia, a cewar Dagamawa.

Ya ce mata da yara na daga waɗanda suka mutu, yana mai ƙarawa da cewa ana ci gaba da neman waɗanda suka tsira.

Mummunan yanayi

Wasu hotuna da kafa yaɗa labaran gwamnati Fana Broadcasting Corporate ta yaɗa a Facebook sun nuna daruruwan mutane kusa da inda lamarin ya faru, sun yi buɗu-buɗu da jar ƙasa.

Hotunan sun nuna mutane suna amfani da hannayensu wajen tono waɗanda suka rayu a cikin ƙasa.

Yankin Gofa yana da kimanin nisan kilomita 450 daa babban birnin ƙasar Addis Ababa, kuma sai an yi tafiya awa 10 kafin a kai yankin daga babban birnin.

#