Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Liberiya tsakanin  Shugaba George Weah da jagoran 'yan adawa Joseph Boakai ranar Talata mai zuwa.

Zaben Liberia zagaye na biyu: Weah da Boakai sun samu goyon bayan 'yan takarar da suka sha kaye

'Yan kasar Laberiya za su sake kada kuri'a a ranar Talata a zagayen zabe na biyu tsakanin shugaban kasar George Weah da tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai, bayan fafatawar da aka yi a zaben zagayen farko inda babu wanda ya yi nasarar samun kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada don samun nasara.

Tsohon dan wasan kwallon kafa Weah ya tashi da kashi 43 .83 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben yayin da Boakai ya tashi da kashi 43.44 cikin 100.

Sakamakon 'yar karamar ratar da aka samu tsakanin 'yan takarar biyu da kuma rashin samun dan takara na uku mai karfi da ya biyo bayansu, na nufin za'a sake fafatawa sosai a zagaye na biyu na zabe, a cewar wata kwarariyar mai sharhi kan bututuwan da suka shafi nahiyar Afirka Maja Bovcon wacce ke aiki da kamfanin leken asiri Verisk Maplecroft.

"Sauran kuri'un da suka rage a zagayen farkon sun rabu ne tsakanin ' yan takarkaru 18 wadanda a yanzu suka fita daga cikin zaben. Nasarar karshe za ta kai ga duk wanda ya samu goyon bayan mafi yawan 'yan takarar da aka fitar," in ji Bovcon.

Zaben zagaye na biyu zai zama maimaici irin wanda aka yi a shekarar 2017 inda Weah ya samun goyon bayan jama'a da ya kai shi ga doke Baokai da kashi 61.54 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Daidaitawa

Weah ya yi nasara bisa alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa da inganta rayuwa a kasar wacce ke yankin yammacin Afirka da har yaznu kokarin farfadowa daga yakin basasa guda biyu da aka yi tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003 da kuma annobar cutar Ebola da ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a shekarar 2013 zuwa 2016 a kasar.

Sai dai wasu masu kada kuri'a sun nuna rashin gamsuwa game da yadda Weah ke gudanar da ayyukansa, musamman kan yaki da matsalar cin hanci da rashawa da rashin ayyukan yi da matasa ke fuskanta da hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalar tattalin arziki gaba daya.

Ya kori shugaban ma'aikatan fadarsa da wasu manyan jami’ai biyu bayan da Amurka ta kakaba musu takunkumi kan cin hanci da rashawa.

Weah ya daura alhakin rashin cimma manufofin tattalin arzikin kasar kan bulla cutar Corona da kuma sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Gabanin zaben zagaye na biyu, 'yan takarar biyu sun samu amincewa daga 'yan takarar da suka sha kaye a zagayen farko.

Weah ya samu goyon bayan jam'iyyar CCP ta Alexander Cummings, duk da cewa shi kansa Cummings din na daga tsakiya.

Tashin hankali

"Na zabi Cummings a zaben da ya gabata amma a wannan karon, George Weah zan baiwa kuri'a ta," in ji Martin Sumo, wani mai goyon bayan Cummings.

Boakai ya samu goyon baya daga 'yan takara uku a cikin hudu da suka sha kaye a zagayen farko na zaben.

Mai sharhi kan harkokin siyasa Bovcon ta ce, duk da adadin goyon bayan da Boakai ya samu ba zai kai ga samun a kashi 50 da ake bukata don samun nasara a zaben ba.

Sai dai wani abu duba da za'a iya mai da hankali akai shi ne kashi kusan 6 cikin 100 na kuri'un da aka soke a zagayen farko.

Edward Appleton Jr, wanda ya zo na uku a zagayen farko na zaben da kashi 2.20 cikin 10 na kuri'un da aka kada, ya ba da goyon bayansa ga Boakai a ranar Talata, yana mai cewa ''Yan Liberiya suna bukatar shugabanci da zai samar wa kasar sakamako mai kyau."

An dai gudanar da zagayen farko na zaben cikin lumana duk da cewa an samu tashe-tashen hankula a wasu wuraren sannan an kashe wasu mutane biyu a rikicin da ya shafi zabe.

Bovcon ta ce akwai yiwuwar a fuskanci tashin hankali a zagaye na biyu na zaben.

“A fafutukar da suke yi na tabbatar da sun samu kuri’u, ‘yan takarar biyu za su iya haifar da rarrabuwar kawuna ko kuma hargitsi a sakamakon zaben, kuma yin hakan na iya iya janyo tarzoma a kan tituna,” inji ta.

#