Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi tayi kan kasarsa ta zama mai shiga tsakani a yakin da Isra'ila ke yi da Falasdinu, yana mai bayyana kwarin gwiwar samar da mafita a yakin.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya a shirye take domin zama mai shiga tsakani a rikicin da Isra’ila take yi da Falasdinu bayan ziyarar da ya kai Kazakhstan.
Erdogan ya jaddada irin karfin da Turkiyya ke da shi a matsayin kasa wadda za ta iya tabbatar da tsaro a Gaza, inda ya jaddada matakan tsaro, siyasa, tarihi, da al'adu.
Ya kara jaddada goyon bayan tsare-tsare wadanda za su samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yayin da ya yi watsi da tsare-tsaren da ke kara tsananta wahalhalun da Falasdinawan ke ciki da kuma kara rura wutar rikicin da ake fama da shi.
Yayin da ya duba kan makomar Gaza, Erdogan ya bayyana fatan da ake da ita ga Gaza a matsayin yanki mai zaman lafiya kan iyakokin da aka shata mata a 1967, wanda ta hadu ta zama kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci wadda Gabashin Birnin Kudus zai kasance babban birnin.