Yawaitar ibtila'o'i sakamakon illar sauyin yanayi kamar mamakon ruwan sama da tsananin zafi, sun tirsasa masanan kimiyya neman hanyoyin da za a amfana da waɗannan munanan yanayi da ake shiga.
Daga Firmain Eric Mbadinga
Fusatar yanayi, salon maganar da ake amfani da shi wajen bayyana sakamakon ayyukan dan adam da ke yin mummunan tasiri kan duniya, ya bayyana a baya-bayan nan ta hanyar afkuwar ibtila'o'i - daga ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a Afirka da suka janyo mutuwa ko raba dubunnan mutane da matsugunansu, zuwa guguguwar da ta afku a Dubai tare da smaun ruwan saman watanni 18 a awanni 24.
Kenya, Tanzania, Burundi, rwanda, Somalia da Ethiopia duk sun fuskanci ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a 'yan watannin nan, inda masanan kimiyya ke cewar sauyin yanayi ne babban dalilin da ya janyo afkuwar wadannan ibtila'o'i da ake yawan samu.
A lokacin da ambaliyar ruwan ta fara ja da baya, sai guguwar Hidaya ta kunna kai gaɓar tekunan Kenya da Tanzania a ranar 4 ga Mayu, tare da janyo mummunar asara a kasashen na Gabashin Afirka. Akalla rayuka 400 aka rasa tare da janyo asarar dukiyoyi na miliyoyin daloli.
To, mene ne kimiyya ke son yi baya ga rage radadin da sauyin yanayi ke janyo wa - har ma da kokarin ganin an ayi amfani da hakan wajen samun ruwa da makamashi?
Abu ne da kamar ba zai yiwu ba, wannan ne tunanin da masana kimiyya ke yi a lokacinda ibtila'o'i ke afkuwa daya bayan daya a cikin watanni.
Sabbin dabaru
Kwararru na alakanta mamakon ruwan sama, ruwan sama a lokacin da ba na damuna ba a wasu yankunan Kudancin Amurka da nahiyar Afirka da guguwar El Nino.
"El Nino na afku wa a lokacinda ruwan Tekun Pacisific ya yi dumi sannan kuma iska ta fara kadawa daga bangaren gabas, inda yanayi ke kara zabi a bangaren duniya daga arewa, tare da daduwar ruwan sama a Kudancin Amurka da kudancin Afirka," in ji Dr George Mwaniki, shugaban kula da ingancin iska a WRI Africa.
A yayinda El Nino da sauran 'btila'o'in da ke da alaka da sauyin yanayi ke ci gaba da zama babbar barazana ga bil'adama, nazarin kimiyya ya samar da dabarun da za iya amfani da mamakon ruwan sama da tsananain zafi don samar da tsaftataccen ruwa da makamashi.
Amfanin wadannan dabaru shi ne don a amfana da yawaitar ruwa da zafin da ake samu, kamar dai yadda wasu suka samar da ruwan sama a sahara.
Masanan kimiyya sun gamsu cewa irin wadannan bincike da dabaru na iya bayar da kariya ga illolin da sauyin yanayi ke haifarwa, su kuma kai ga samar da hanyar rarraba arziki a duniya da hanya mafi adalci.
Jovanie Sonie Ndong Songo, masanin gine-gin da tsara birane a gabon, na da ra'ayin cewa dole ne a samar da ingantaccen tsarin tsara birane a kasashen Afirka kafin samar da fasahar amfani da mamakon ruwan sama da tsananin zafi don amfanin dan adam.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Baya ga yaki da sauyin yanayi, akwai kuma batun amfani da filaye da samar da dabarun kaucewa fuskantar danja. Ibtila'o'in baya-bayan nan a Kenya da wasu kasashen Afirka sun nuna muhimmancin samar da kyawawan magudanan ruwa da tsarin tunkarar matsalolin gaggawa."
"Yana da muhimmanci a kirkira tare da tsara sabbin hanyoyi da za su dinga rike ruwan sama da wanda ba na sama ba a waje guda."
Dabarun kimiyya masu yawa
Dabarar da Jovanie ya kawo, wadda ake kira da madatsar mamakon ruwan sama, ta yi nasara sosai a kasashe irin su Canada. Bayan ambaliyar ruwan 2011 da Tafkunan Champlan da Richelieu suka janyo, wnai bincike ya bayar da shawarar cire dukkan katangun da ake da su.
Charlene Mouboulou, 'yar jarida kuma injiniyar kula da muhalli, ta bayar da shawarar cewa kasashe za su iya kirkirar madatsun ruwa don rike ruwan, ko su kirkiri tafkunan da babu su, duba da yanayin yadda kasa da yankin suke, domin amfani da ruwan nasu.
"Za a iya amfani da ruwan da ke zuwa daga wadannan madatsun don gine-gine, ayyukan jama'a, noma da kiwon kifi, ko ma a gidaje. Duk wadannan bangarori na bukatar ruwa sosai," ta shaida wa TRT Afirka.
Hassan Chouaouta, abokin aikinta daga Morocco kuma Shugaban Cibiyar Cigaba Mai Dorewa ya ce za a iya amfani da duk wani yawaitar gangarowar ruwa da madatsu don samar da makamashin lantarki.
"Za mu iya sauya wannan matsala a amfana da ita. na yi amanna cewa garuruwa na bukatar kayan more rayuwa da z asu maance afkuwar wani ibtila'i, amma mafi muhimmanci shi ne a samu damar kawar da ambaliyar ruwa zuwa tafkuna da wuraren da za a iya ajje su ba tare da wata matsala ba," in ji Chouaouta.
"Za mu iya samar da lantarki daga ruwa, mu yi amfani da wannan ibtila'i don cigabanmu."
Amfana da tsananin zafi
Kafin ambaliyar ruwan baya-bayan nan, watanni shida na biyu na 2023 sun shaida karuwar zafi a yanayin duniya, wanda ke janyo fari a wasu yankunan da wutar daji a wasu.
A jihar California ta Amurka, zafi ya taba kai wa 54°C, wanda ke nufin za a iya soya kwai a kan kwalta. tsananin zafin ya kuma janyo asarar rayuka da dama.
A 2020, a lokacin da tsanantar zafin ya kai makura, Dr Mikael Philippe na Ofishin masu Bincike Kan Yanayi a Faransa na shirin samar da cibiyar samar da makamashi daga sararin duniya a matsayin hanyar sanyaya gidaje.
Dr Philippe ya bayyana fasahar samar da makamashi daga sararin duniya a matsayin "kimiyyar da ke nazari kan zafin da duniya ke kunshe da shi da kuma fasahar bayar da damar amfana da zafin".
Mouboulou ya bayar da shawarar amfani da muhimmin sauyi zuwa ga fasahar amfani da hasken rana. "Za mu iya amfani da wannan makamashi don fadada ayyukan noma. Wasu yankunan ba za su iya samar da wasu kayan amfanin gona ba saboda yanayinsu," in ji ta.
A yankunan da ba sa samun ruwan sama sosai, ana amfani da dabarar narka gajimare don kawo ruwa daga yankunan da suke da shi sosai.
A shekarar 1948 ne dan kasar Amurka Charles Mallory Hatfield ya kirkiri wannan fasaha tare da ba ta sunan "mai yin ruwan sama". Ana zuba wani irin sinadari na aerosol da buraguzan kankara a kan gajimaren da suke komawa su zama ruwa. Dubai na amfani da wannan fasaha tsawon shekaru.