Yayin da rashin zaman lafiya ke damun hanyar Tekun Fasha da Iraki ke fitar da kayayyaki ta cikinta, Baghdad na juyawa ga arewa, tana fitar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙkasa da ƙasa ta cikin Turkiyya.

Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa

Turkiyya na ci gaba da tasowa a matsayin babbar madadin hanyar fitar da mai daga Iraƙi zuwa kasuwannin duniya a yayin da yaƙin Amurka, Isra’ila da Iran ke ci gaba da kawo cikas a Mashigar Teku ta Hormuz.

A halin yanzu Iraki tana fitar da kusan ganga miliyan 2.6 a kowace rana daga tashoshin jiragen ruwanta na kudu, kuma tana samar da sama da ganga miliyan uku a kowace rana daga rijiyoyin kudu, in ji Bassem Abdul Karim, shugaban Kamfanin Man Fetur na Basra a ranar Alhamis.

A yanzu haka ana jigilar kimanin ganga 250,000 na ɗanyen mai na Basra zuwa Kirkuk kafin shiga hanyar bututun mai ta arewa da kuma isa tashar jiragen ruwa ta Ceyhan ta Bahar Rum da ke Turkiyya.

Yawan man ya kasance kaɗan idan aka kwatanta da yawan man da Iraƙi ke samarwa, amma sauyin ya jawo hankali ga bututun mai na Kirkuk-Ceyhan da aka daɗe ana amfani da shi a matsayin madadin hanyar fitar da shi ga kasuwannin ƙasa da ƙasa.

Daga Basra zuwa Ceyhan

Iraƙi ta ƙaddamar da wani gwaji a watan Satumba don jigilar mai ta hanyar mota daga rijiyoyin mai na kudancin ƙasar zuwa wuraren ajiya da ke Kirkuk.

Wannan aikin, wanda Kamfanin KAR na Iraƙi ke gudanarwa, yana amfani da manyan motocin tankuna don ɗaukar mai daga arewa kafin a tura shi ta hanyar bututun mai na arewa zuwa Turkiyya.

A lokacin gwajin farko na kwanaki biyu, manyan motocin tankuna 209 sun yi jigilar mai fiye da lita miliyan shida daga kudancin Iraƙi zuwa Kirkuk.

Aikin ya dogara ne a kan ƙoƙarin da aka fara a farkon wannan shekarar.

An yi jigilar kimanin ganga 90,000 na man fetur daga Basra zuwa arewa a watan Afrilu. Adadin ya ƙaru zuwa ganga 140,000 a watan Mayu kafin ya kai kusan ganga 250,000 a watan Satumba.

Faɗaɗawar da aka yi cikin sauri ta nuna ƙoƙarin da Baghdad ke yi na haɗa manyan rijiyoyin haƙar mai na kudancin ƙasar da hanyar fitar da mai daga arewacin da ke kaucewa Tekun Gulf.

A tsakiyar hanyar akwai bututun mai na ɗanyen mai na Iraki-Turkiyya, wanda aka fi sani da bututun Kirkuk-Ceyhan.

An gina bututun a shekarun 1970, wanda ya haɗa arewacin Iraki da Ceyhan a bakin tekun Bahar Rum na Turkiyya. Ƙarfin aikinsa ya kai har ganga miliyan 1.6 a kowace rana, kodayake yawan man da ke bi ta cikinsa ya kasance ƙasa da wannan adadi a tarihi.

Wurin da Ceyhan yake na ba wa Iraƙi wata muhimmiyar fa'ida: jiragen ruwa da ke tashi daga tashar za su iya shiga Bahar Rum kai-tsaye ba tare da sun ratsa ta Mashigar Hormuz ba.

Turkiyya da Iraki sun zurfafa kawance a fannin makamashi

Ankara da Baghdad sun kuma ɗauki matakai don faɗaɗa hanyar.

A ranar 1 ga Agusta, Turkiyya da Iraƙi sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta shekara ɗaya da nufin haɓaka amfani da bututun mai yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan tsarin makamashi na dogon lokaci.

Yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawa tsakanin Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar da Ministan Man Fetur na Iraki Basim Mohammed Khudair.

A ƙarƙashin wannan shiri, Iraki ta yi alƙawarin ƙara yawan man da ke shiga bututun daga kusan ganga 220,000 a kowace rana zuwa ga garantin ƙarfin ganga 750,000 a kowace rana yayin da samar da mai a kusa da Kirkuk ke faɗaɗa.

Bayraktar ya ce bututun man ya zama mai muhimmanci ga tsaron makamashi na yanki da na duniya, yana mai bayyana rawar da Turkiyya ke takawa wadda take fiye da jigilar man fetur na Iraki kawai.

Haɗin gwiwar kuma yana ci gaba da tafiya. Kamfanin Man Fetur na Turkiyya TPAO, ya sami hannun jari a fannin man fetur na Kirkuk da ke ƙarƙashin ikon BP na Iraki, yana faɗaɗa haɗin gwiwar makamashi tsakanin ƙasashen biyu zuwa samar da mai a tsandauri.

Jami'an Iraki sun sha alwashi kan wani babban buri na samar wa Turkiyya mai har zuwa ganga miliyan ɗaya a kowace rana.

Girmamar rawar da Ceyhan ke takawa

Fadada wannan hanya ya ƙara daga muhimmancin Ceyhan a yanzu a matsayin cibiyar makamashi ta duniya.

Tashar jiragen ruwa ta Turkiyya ta riga ta zama ƙarshen bututun mai na Baku-Tbilisi-Ceyhan, wanda ke ɗaukar ɗanyen mai na Azerbaijan ta hanyar Georgia da Turkiyya.

Ƙaruwar samar da mai daga tashar mai ta Gabar ta Turkiyya ta ƙara wani tushen mai na cikin gida zuwa Ceyhan.

Jami'an Turkiyya sun kuma tattauna faɗaɗa haɗin gwiwa da Iraki bayan mai zuwa iskar gas da wutar lantarki, yayin da Ankara ke ganin hanyar a matsayin ƙarin faffadan Aikin Hanya na Ci Gaba da ke haɗa Tekun Gulf da Turai ta hanyar Iraki da Turkiyya.

Jigilar dubunnan ɗaruruwar ganga da ya fi rikitarwa fiye da jigilar ɗanyen mai kai tsaye ta bututu, wanda hakan ke sa ƙarin jarin kayayyakin more rayuwa ya zama mai muhimmanci idan yawan ya ci gaba da ƙaruwa.

Duk da haka, canjin jigilar man ta bututu ruwa yana nuna muhimmancin da Turkiyya ke da shi ga dabarun sayar da makamashin Iraki.

Hanyar da aka ƙirƙira kusan rabin ƙarni da ya gabata tana sake bai wa Baghdad damar shiga Bahar Rum, yayin da Ceyhan ke ƙarfafa matsayinta a matsayin ƙofar da za ta haɗa ɗanyen mai na Iraki da kasuwannin duniya.

#