Yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 150 - ya kashe Falasɗinawa aƙalla 30,410, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 71,700.

Ya kamata Falasdinawa su yi fito na fito da Isra'ila a lokacin azumin Ramadan — Hamas

1332 GMT — Ya kamata Falasdinawa su yi fito na fito da Isra'ila a lokacin azumin Ramadan — Hamas

Hamas na kira ga Falasdinawa a Isra'ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da su tashi tsaye don nuna adawa da mamayar Isra'ila a cikin watan Ramadan mai alfarma da ke gabatowa.

Mai magana da yawun ƙungiyar Hamas, Osama Hamdan, da yake zantawa da manema labarai a birnin Beirut, ya ce Falasdinawa su sanya kowane lokaci na watan Azumin ya zamo wata arangama.

Kasashen Amurka da Qatar da Masar dai sun kwashe makonni suna kokarin ganin an tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza da kuma shawo kan kungiyar masu fafutukar ganin an sako wasu adadi mai yawa na mutanen da ake garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

1237 GMT — An kama mutane da dama a sabon farmakin da Isra'ila ta kai a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye

Sojojin Isra'ila sun kama wasu Falasdinawa 55 a farmakin da sojojin suka kai a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da suka mamaye, a cewar kungiyoyin da ke kula da fursunoni.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da hukumar kula da fursunonin Falasdinawa ta fitar ta ce, an kai aƙalla mutum 22 hannun Isra'ila a birnin Hebron, yayin da wasu kuma aka kama su a garuruwan Bethlehem da Ramallah, da ke Gabashin Kudus da kuma Qalqilya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kamen na nuni da ayyukan zagon ƙasa da lalata gidajen ‘yan kasar, baya ga mummunan duka da ake yi wa fursunonin da iyalansu, da kuma ƙwace kuɗaɗe.

0740 GMT — Ministan Isra'ila ya yi kira da a taƙaita shigar Musulmai Masallacin Ƙudus a cikin watan Ramadan

Ministan Tsaron Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben Gvir, ya buƙaci ƴan sanda da su taƙaita shigar Musulmai Masallacin Ƙudus a cikin watan Ramadan mai alfarma, kamar yadda kafar yada labaran Isra'ila ta bayyana.

A yayin ganawar tasu, Ben Gvir ya shaida wa kwamishinan ‘yan sanda Kobi Shabtai da ya taƙaita yawan masu ibada a Ƙudus domin tabbatar da cewa ‘yan sanda sun shirya yin gaggawar mayar da martani ga duk wani hargitsi, kamar yadda jaridar Maariv ta Isra’ila ta ruwaito.

Jaridar ta kuma bayyana cewa, a ranar Litinin ne ake sa ran Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai tattauna batun hana shiga Masallacin Ƙudus tare da Ben Gvir Shabtai, da jami'an hukumar tsaro ta Shin Bet da kuma sojojin Isra'ila.

0836 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya haura 30,534 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare

Aƙalla Falasɗinawa 30,534 aka kashe a yayin yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta yankin da aka yi wa ƙawanya ta faɗa.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce aƙalla mutum 124 ne suka mutu yayin da wasu 210 suka jikkata a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayin da wasu 71,980 suka samu raunuka tun bayan yakin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba bayan harin Hamas.

Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa, Isra'ila ta aikata kisan kiyashi 13 a Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

0236 GMT — Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin wani abu mai muni.

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.

A yayin wani jawabi da ta yi a Alabama na tunawa da shekaru 59 na "Lahadin da aka Zubar da Jini," ranar da jami'an gwamnatin jihar suka kai wa masu zanga-zangar kare hakkin jama'a hari a gadar Edmund Pettus da ke Selma, Harris ta ce tsagaita wutar za ta bayar da damar fitar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma ba da damar shigar da taimakon da ake bukata a Gaza.

Ta ƙara da cewa, "Kuma idan aka yi la'akari da ɗimbin wahala a Gaza, dole ne a tsagaita wuta nan da nan na aƙalla makonni shida masu zuwa, kuma a halin yanzu wannan batu yana kan teburin tattaunawa."

"Wannan zai ba mu damar gina wani abu mai ɗorewa don tabbatar da cewa Isra'ila ta kasance cikin tsaro da kuma mutunta ƴancin al'ummar Falasɗinu na mutunci da ƴanci na cin gashin kai," in ji ta.

0040 GMT Sojojin Isra'ila sun kashe sama da Falasɗinawa 127 a wajen karɓar fulawa a Gaza

A baya-bayan nan ne sojojin Isra'ila suka kashe Falasɗinawa sama da 127 tare da jikkata sama da 760 a cikin kwanaki biyu kacal ta hanyar kai hari kan fararen-hula da ke ƙoƙarin karɓar agajin jinƙai, duk da cewa kotun duniya ta ICJ ta umarci Isra'ila da ta inganta yanayin jinƙai a Gaza.

Ko da yake a ranar Alhamis ɗin da ta gabata sojojin Isra'ila sun buɗe wuta kan taron Falasɗinawa da ke jiran manyan motocin dakon kaya a unguwar Al Nabulsi da ke Kudancin Gaza.

Kotun ta ICJ ta yanke hukunci kan taƙaddamar da ke tsakanin jihohi kuma umarninta na da nasaba da doka, amma ba ta da hanyar tabbatar da aiwatar da hukunce-hukuncenta.

Sojojin Isra'ila sun yi iƙirarin cewa mutanen ne suka tunkari sojojinsu, lamarin da suke ganin zai jefa su cikin haɗari, don haka suka mayar da martani ta hanyar buɗe wuta.

#