Danielle Aloni ta rubuta wata wasika mai ratsa jiki inda ta nuna godiya ga mayakan Hamas bisa kulawar da suka bai wa diyarta Emilia a zaman da suka yi na kwanaki 49 ana garkuwa da su a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Danielle Aloni da ƴarta Emilia ƴar shekara biyar, sun shafe kwana 49 a tsare a hannun ƙungiyar Hamas a matsayin waɗanda ake garkuwa da su a yankin Gaza da aka yi ƙawanya.
A ranar 24 ga watan Nuwamba, aka saki uwar ƴar Isra'ila da ƴarta a cikin shirin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila, inda suka haɗu da danginta.
Kafin su bar Gaza, sai da Danielle Aloni ta rubuta wasiƙar "godiya" ga Hamas, tana cewa, "Ina gode muku daga ƙololuwar zuciyata saboda irin tausayin da kuka nuna wa ƴata, Emilia."
Rundunar Qassam, wadda ita ce rundunar ƙungiyar Hamas, ta wallafa wasikar a shafinta na Telegram da karfe 1649 GMT a ranar 27 ga Nuwamba.
An rubuta wasikar a asali da harshen Ibrananci wacce aka wallafa ta tare da fassarar Larabci, da hoton Ba’isra’ilayar uwar da ’yarta.
'Na zama tamkar sarauniya'
A cikin wasiƙar da ta rubuta cikin Ibrananci, Danielle ta ce: “Ita (Emilia) ta yarda cewa ku duka abokanta ne, ba ma abota ba kawai, amma haƙiƙanin abin ƙauna ne."
Kazalika Aloni ta yabi Hamas kan irin kyakkyawar kulawar da ta ba su a matsayin waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, inda ta rubuta cewa: "Mun gode da tsawon lokacin da muka shafe tare da ku kuna kula da mu."
Ta kuma ƙara da cewa bayan sabon da ƴarta ta yi da ƴan ƙungiyar Hamas, ta kuma dinga jin ta tamkar sarauniya.
"Bai kamata a dinga yin garkuwa da yara ba, amma muna gode muku da ma sauran mutane masu kirki da muka haɗu da su a wannan tafiyar, ƴarta ta dinga jin ta tamkar sarauniya a Gaza," ta ce.
A dogon zaman da muka yi ba mu hadu da wanda bai kyautata mata ba, kun zauna da ita cikin kyautayi da jinƙai da tausayi.
Aloni ta kawo karshen wasiƙarta da nuna tausayin Hamas, tana mai cewa: “Zan dinga tunawa da halin kirki da kuka nuna mana duk da halin ƙuncin da kuka fuskanta da kuma asarar da kuka tafka a nan Gaza."
"Ina fata a cikin duniyar nan da gaske mu zama abokai na ƙwarai," ta rubuta kuma ta ƙara da fatan alheri ga al'ummar Gaza "Ina yi muku fatan lafiya da zama lafiya... lafiya da soyayya a gare ku da iyalanku.
Danielle da Emilia Aloni na daga cikin ‘yan Isra’ila 24 da Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 24 ga Nuwamba. Sun ne ziyartar ‘yar uwar Danielle da danginta ne a Kibbutz Nir Oz da ke kudancin Isra’ila kafin a yi garkuwa da su.