Manyan malaman Musulunci a India sun shirya zama dirshan da zanga-zanga da kuma kamfe a shafukan sada zumunta don neman sauya dokar Waƙafi da suke ganin ba ta dace ba.

Ƙungiyar Musulmai za ta yaƙi sauya dokar Waƙafi a faɗin Indiya

Wata babbar Ƙungiyar Musulmai ta All India Muslim Personal Law Board a Indiya, ta sanar da wani gagarumin yakin neman goyon baya a fadin kasar kan wata doka da aka gabatar da za ta ƙara wa gwamnatisamun iko a kan ƙadarorin Waƙafi.

Waƙafi na nufin filaye ko kadarori da wani Musulmi yake bayarwa don dalilai na addini ko ilimi, ko kuma ayyukan alheri.

Syed Qasim Rasool Ilyas, mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana cewa kwamitin ayyuka mai mambobi 31 na kungiyar ya yanke shawarar amfani da dukkan hanyoyi na “doka da tsarin mulki, da dimokuradiyya” don kalubalantar abin da suka kira doka mai “rikitarwa da nuna bambanci, da kuma cutarwa.”

Kungiyar ta tsara shirin zanga-zanga a fadin kasar, ciki har da gudanar da jerin gwano a dukkan manyan biranen jihohi, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar a daren Lahadi ta bayyana.

“A matsayin wani bangare na matakin farko na wannan fafutuka, an shirya gudanar da zaman dirshan na zanga-zanga a gaban majalisun jihohi a Patna da Bihar a ranar 26 ga Maris da kuma a Vijayawada a ranar 29 ga Maris,” in ji Ilyas.

‘Wannan ba Dimokuradiyya ba ce’

Yakin neman goyon bayan zai hada da zaman dirshan da zanga-zanga da kuma amfani da kafafen sada zumunta, musamman amfani da maudu’i a shafin X, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Bugu da ƙari, za a shirya tarukan jama’a da tarukan bita da muhawara, da zaman dirshan a matakin ƙananan hukumomi, sannan za a miƙa takardun koke ga Shugaban Ƙasar Indiya ta hannun shugabannin kananan hukumomi,” in ji sanarwar.

Dokar, wadda ta fara fuskantar adawa daga jam’iyyun hamayya, an miƙa ta ga wani kwamitin hadin gwiwa na ‘yan majalisa, wanda yanzu ya gabatar da rahotonsa. Ana sa ran za a sake gabatar da dokar a zaman majalisar da ake yi yanzu.

Duk da cewa ƙungiyar Musulman ta bayyana cewa al’ummar Musulmi sun yi watsi da dokar gaba daya a matsayin “wanda ba dimokuradiyya ba,” jam’iyyar Bharatiya Janata Party mai mulki, karkashin jagorancin Firaminista Narendra Modi, ta ce dokar na nufin tabbatar da “adalci da gaskiya.”

A ranar 17 ga Maris nw kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a New Delhi kan gyare-gyaren da aka gabatar.

#