Kasar Turkiyya na ƙoƙarin ganin ƙasashen Musulmai na duniya za su ɗauki matakin haɗin gwiwa kan zaluncin da ake yi a Gaza, in ji Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Turkiyya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin daƙile zalunci a Gaza: Shugaba Erdogan

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen dakatar da "zalunci a Gaza da Falasɗinu da kuma cin zarafi da Isra'ila ke yi."

"Za mu yi amfani da duk wata hanya da za mu bi, ba tare da wani tsoro ba, wajen kawo ƙarshen zaluncin da ake yi a Gaza da kuma muzgunawa Birnin Ƙudus," in ji Erdogan a wani gangamin da aka yi a lardin Balikesir da ke yammacin Turkiyya a yau Juma'a.

Ya kuma ƙara da cewa, Turkiyya na ƙoƙarin ganin ƙasashen Musulmai na duniya sun ɗauki matakin haɗin gwiwa kan zaluncin da ake yi a Gaza.

Dangane da yunƙurin Turkiyya na yaƙi da ta'addanci, Erdogan ya ce Ankara za ta ƙaddamar da ayyuka don daƙile tare da tarwatsa yunƙurin kafa daular ta'addanci a kudancin iyakarta da arewacin Siriya.

“Tare da sabbin ayyuka, za mu ci gaba da ruguza aikin kafa ƴan ta’adda ta hanyar kewaye ƙasarmu daga kan iyakokinta na kudanci,” in ji shi.

#