Dollar

40,3901

-0.01 %

Euro

47,3184

0.57 %

Gram Gold

4.412,4100

1.42 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ankara ta fitar da jerin matakan siyasa da tattalin arziki da shari’a kan Isra’ila yayin da take watsi da labaran ƙarya da ke neman yin zagon ƙasa ga goyon bayan da ta daɗe tana yi wa gwagwarmayar Falasɗinawa.

Turkiyya ta yi watsi da iƙirari kan manufarta a Falasɗinu, ta nanata goyon bayanta ga adalci a Gaza

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta yi watsi da zarge-zargen da ke neman sa shakku kan matsayarta game da Falasɗinu, tana mai bayyana su a matsayin labarai “mara tushe bare makama” kuma matakai na siyasa na neman karkata gaskiya da kuma rinjayar ra’ayin jama’a bisa rashin gaskiya.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ma’aikatar ta ce, “jerin iƙirarin da aka yi kwanan nan kan manufar ƙasarmu game da Falasɗinu ba su dace da gaskiya ba. Mun yi watsi da ƙoƙarin aibata goyon bayan Turkiyya ga Falaɗinawa ta ajandar siyasa da yaɗa ƙarya.”

‘Matsaya mafi ƙarfi da ke adawa da kisan kiyashi a Gaza’

Turkiyya tana ci gaba da wata “manufa mai cin gashinkanta kuma mai adalci game da batun Falasɗinu,” kamar yadda ma’aikatar ta jaddada, tana mai ƙarawa da cewa Ankara ta kasance cikin waɗanda suka fi sukar yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza.

“Turkiyya ta ɗauki matsaya mafi ƙarfi wajen adawa da kisan kiyashin da Isra’ila take yi a Gaza,” in ji sanarwar. “Yadda ‘yan siyasar Isra’ila suke sukar Turkiyya a ko wace damar da suka samu hujja ce ta dacewar manufarmu mai ƙa’ida.

Saɓanin iƙirarin ƙarya da ake yi, ma’aikatar ta bayyana cewa Turkiyya ta aiwatar da matakai da suka zarce shawarwarin da aka rubuta a cikin sanarwar ƙarshen taro da aka fitar a Bogotá daga farko a cikin wannan shekarar. Ta yi tuni da cewa Turkiyya ta dakatar da kasuwanci gaba ɗaya da Isra’ila a watan Mayun shekarar 2024, ciki har da dukkan shige da ficen kayayyaki.

“Yayin aiwatar da wannan shawarar, mun yi taka-tsantsan domin tabbatar da cewa ba ta yi mummunan tasiri kan ‘yan’uwanmu Falasɗinawa ba,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.

Katse cinikin soji, jagorantar shirin Majalisar Ɗinkin Duniya

Turkiyya ta kuma ɗauki matakai na hana sayar da duk abu mai alaƙa da soji ga Isra’ila, in ji ma’aikatar. Ta kuma taka rawa ta gaba-gaba a matakan duniya na hana kai makamai Isra’ila, ciki har da jagorantar wani shirin a Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashe 52 suka mara wa baya.

Ma’aikatar ta jaddada cewa tana bibiyar batun jirgin ruwan kayayyakin agaji na Madleen tare da yin Allah wadai da “matakin da ya ƙeta doka” da Isra’ila ta ɗauka a cikin tekun ƙasa da ƙasa. “An ɗauki dukkana matakan diflomasiyya domin tabbatar da cewa na sake ‘yan ƙasarmu da ke cikin jirgin,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Tallafin sake gina Gaza da kuma matakin shari’a

Ankara ta jaddada adawarta ga dukkan shirye-shiryen da ke ƙunshe da tilasta wa Falasɗinawa barin Gaza. Ta nanata goyon bayanta ga shirin haɗaka na Ƙungiyar ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Haɗinkan ƙasashen Musulmi na sake gina Gaza, da kuma sauran matakai na ƙasashen duniya na daƙile irin waɗannan shirye-shiryen tilasta ƙauran.

A ta fannin shari’a kuwa, Turkiyya ɗaya ce daga cikin ƙasashe 13 da suke da hannu a ƙarar kisan kiyashi da aka shigar kan Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka (ICJ), kamar yadda ma’aikatar ta jaddada. Ta kuma ba da gudumawa a zaman shawara biyu a kotun.

Turkiyya ta ci gaba da neman adalci wa Aysenur Ezgi Eygi, wadda sojojin Isra’ila suka kashe,  kuma ta jaddada goyon bayanta na diflomasiyya bayan an saki ‘yar Turkiyya Rumeysa Ozturk, wadda hukumomin shige da ficen Amurka suka tsare.

“Turkiyya ba za ta ƙyale wani matsi ko ɓata suna ya raunata matsayarta ta adalci ba,” in ji ma’akatar harkokin wajen. “[Wani abu] mai tushe a son gaskiyar ƙasarmu, wannan yaƙin neman adalci zai ci gaba ba kakkautawa bisa dokokin ƙasa da ƙasa da ‘yancin ɗan Adam.”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#