Sabuwar dokar Turkiyyar, wadda za ta fara aiki ranar 1 ga watan Nuwamba, na buƙatar tantance shekaru ta shafin gwamnati mai ɗauke da bayanan 'yan ƙasa na e-Devlet tare da hana kafafan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekaru 15 hidima.
Shafin gwamnatin Turkiyya ya wallafa wata sabuwar doka ranar Asabar kan tabbatar da shekarun masu amfani da shafukan sada zumunta, inda ta hana shafukan sada zumunta bai wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 damar amfani da su.
A ƙarƙashin dokar, wadda ɓangaren tsaron intanet na fadar shugaban ƙasar ya tsara, za a tabbatar da shekaru ne ta hanyar shafin gwamnati mai ɗauke da bayanan ‘yan ƙasa wato e-Devlet.
Ba za a bai wa kamfanonin shafukan sada zumunta damar yi wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 hidima ba. Shafukan yara da suka riga suka cika shekara 15 kuwa za a ba su wasu saƙonnin ne kawai da suka fi dacewa da matakin girmansu na zahiri da tunani da ƙwakwalwa da kuma zuciya.
Dokar na buƙatar shafukan su ayyana tsarin kare sirri mai tsauri ka shafukan yara, su ayyana su a matsayin na sirri da kuma hana su iya watsa bidiyo kai tsaye da kuma talla na musamman dominsu.
Kazalika dole shafukan sada zumuntan su tabbatar da cewa yara za su iya karɓar saƙonnin ne kawai daga shafukan da suke bi, kuma a ɓoye mabiyansu da waɗanda suke bi daga sauran masu amfani da shafukan.
An kuma buƙace su su ba da iko da iyaye za su iya amfani da su wajen taƙaita tsare-tsaren shafukan yaransu da kuma ikon amincewa da cinikayya a shafukan yaran.
Dokar za ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Nuwamba. Dole a tantance shekaru na shafukan da ke aiki a yanzu zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2027, kuma za a rufe shafukan da aka gane cewa na ‘yan ƙasa da shekaru 15 ne.
