Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai halarcitaron BRICS a Kazan, inda ya bayyana aniyarsu na karfafa alaka da kungiyar.
Turkiyya na bukatar habaka alakar kasar da kawancen BRICS, kuma za ta halarci taron ranar Laraba sakamakon gayyatar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wa kasar, in ji shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Jawabin Erdogan na ranar Talata na zuwa ne a lokacin da Rasha ta shirya karbar bakuncin Taron Shugabannin kasashe mambobin kawancen BRICS a birnin Tatarstan na Kazan.
"Kasashen BRICS, wani bangare mai muhimmanci na G20 kamar Turkiyya, suna da kusan kashi 30 na fadin kasa na duniya da kuma kashi 45 na yawan jama'ar duniyar," in ji Erdogan.
Ya yi tsokaci da cewa kasashen BRICS ne ke da kashi 45 na yawan jama'ar duniya, kuma suna fitar da kashi 40 na albarkatun mai a duniya inda suke fitar da kashi 25 na kayayyaki a duniya.
"A matsayin mu na Turkiyya, muna son karfafa alakarmu da BRICS," in ji Erdogan.
Turkiyya a taron BRICS
Da fari a ranar Litinin, mai bayar da shawara ga shugaba Putin, Anton Kobyakov ya gana da jakadan Turkiyya a Moscow Tanju Bilgic kuma dukkan bangarorin biyu sun tattauna kan yadda wakilan Turkiyya za su halarci taron na BRICS.
"Tawagar Turkiyya za ta halarci taron BRICS a babban matsayi, kuma babbar shaida ce ta sha'armu na shiga kawnacen. Ba ni da tantama cewa wannan hadin kai zai samar da karin damarmaki na fadada alaka," in ji Bilgic.
Dukkan bangarorin biyu sun tattauna kan hadin kan tattalin arziki tsakanin Ankara da Moscow, tare da auna bukatar habaka damarmakin zuba jari.
"Kasashenmu a hankali suna karfafa alakarsu a muhimman bangarori. Na yi amanna cewa halartar taron BRICS da Turkiyya za ta yi zai zama babban al'amari da zai bayar da damar samun sabbin bangarorin hadin kai da kuma karfafa dangantaka," in ji Kobyakov.
Taron na kwanaki biyu na BRICS ya kunshi kasashe mambobin kawancen na Barazil, Rasha, India, China da Afirka ta Kudu - wanda su ne suka fara kafa kawancen - daga baya kuma aka shigar da Masar, Ethiopia, Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa ciki.