Sport
Dollar
42,7158
0.04 %Euro
50,2127
-0.01 %Gram Gold
5.890,4900
-0.31 %Quarter Gold
9.757,7100
0 %Silver
86,5900
-1.56 %Ankara ta sake jaddada goyon bayanta wajen neman hanyoyin da za su kasance mafita wurin samar da zaman lafiya a Sudan.
Turkiyya a ranar Litinin ta yi Allah wadai da harin jirgin sama marar matuki da aka kai kan sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan wanda ya kashe sojojin wanzar da zaman lafiya guda shida daga Bangladesh kuma ya jikkata wasu takwas.
“Muna roƙon rahamar Allah ga sojojin wanzar da zaman lafiya na Bangladesh da suka rasa rayukansu a wannan mummunan harin, da kuma samun lafiya a cikin gaggawa ga waɗanda suka ji jikkata,” in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a cikin wata sanarwa.
Ma'aikatar ta jaddada muhimmancin samar da haɗin kai a ƙasar Sudan, tare da jaddada “goyon baya mai ƙarfi ga ƙoƙarin neman mafita ta lumana ga rikice-rikicen da ke ci gaba a ƙasar.”
Harin ya afku ne yayin da rikici tsakanin rundunar sojin Sudan da ƙungiyar sa-kai ta Rapid Support Forces (RSF) ke ci gaba ba tare da raguwa ba. Rikicin wanda aka fara tun Afrilun 2023 ya kashe dubban mutane, sannan ya tilasta miliyoyin mutane barin gidajensu kuma ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen jinƙai a duniya.
Rundunar sojin Sudan ta zargi RSF da kai harin. Babu wani martani nan take daga ƙungiyar ta 'yan tawaye.
Sojojin wanzar da zaman lafiya sun kasance cikin Rundunar Tsaro ta Wucin Gadi ta Majalisar Dinkin Duniya don Abyei (UNISFA), wadda aka tura a yankin iyaka mai arzikin mai da ake takaddama a kai wanda Sudan da ƙasar makwabta Sudan ta Kudu ke gudanarwa.
A makon da ya gabata, Sudan ta Kudu ta sanar cewa ta cim ma yarjejeniya mai ɓangarori uku tare da rundunar sojin Sudan da RSF don sanya tsaro a filin mai na Heglig — wanda ke a Kordofan ta Yamma, kusa da iyaka tsakanin kasashen biyu — a ƙarƙashin kulawar Sojojin Kare Mutanen Sudan ta Kudu (SSPDF).
Yarjejeniyar ta bai wa SSPDF “babban alhakin tsaro” kan wuraren mai a Heglig.
An sabunta ikon aikin UNISFA a watan da ya gabata.
Comments
No comments Yet
Comment