Shugaban Nijar Abdourahamane Tchiani ya ziyarci cibiyoyin ROKETSAN a Ankara domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijar da Türkiye.
ANKARA
Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, tare da tawagarsa sun kai ziyara cibiyoyin kamfanin ROKETSAN yayin ziyararsu ta hukuma a Türkiye.
A lokacin ziyarar, an gabatar wa tawagar bayanai kan fasahohin tsaro na cikin gida da Türkiye ke samarwa, ƙarfin masana’antu, ayyukan bincike da ci gaba, da kuma manufofin ci gaban masana’antar tsaro a nan gaba.
Bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar da ake da shi a yanzu tare da gano sabbin damar haɗin kai a fannin tsaro da ci gaban fasaha.
Shugaban Hukumar Masana’antar Tsaro ta Türkiye, Farfesa Dakta Haluk Görgün, ya bayyana cewa ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron Nijar tare da ƙara bunƙasa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen.
A ƙarshen ziyarar, ɓangarorin biyu sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da sauran muhimman fannoni na dabarun ƙasa da ƙasa.

