Dollar

42,0958

0.24 %

Euro

48,6520

-0.18 %

Gram Gold

5.413,4200

-0.31 %

Quarter Gold

9.254,6300

0.46 %

Silver

65,8700

-0.26 %

Shugaban ƙasar ya ce, duk wani bayani da ke nuna cewa Nijeriya ƙasa ce mai fama da tsatsauran ra’ayin addini, ba ya nuna ainihin gaskiyar abin da ke faruwa, kuma ba ya la’akari da ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da ‘yancin addini da ra’ayi ga kowa.

Tinubu ya mayar da martani bayan Amurka ta ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasar da ake mulkin dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan bangarorin addinai, in ji shugaban a wata sanarwar.

Sanarwar ta Tinubu wadda aka fitar a ranar Asabar na zuwa ne bayan Amurka ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga kowane yanki da addini.

“Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini,” in ji Tinubu.

“Tun daga 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai daban-daban da yankuna.”

Shugaban ƙasar ya ce, duk wani bayani da ke nuna cewa Nijeriya ƙasa ce mai fama da tsatsauran ra’ayin addini, ba ya nuna ainihin gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasa, kuma ba ya la’akari da ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da ‘yancin yin addini da ra’ayi ga kowa da kowa.

“‘Yancin addini da haƙuri suna daga cikin ginshiƙanmu kuma za su ci gaba da kasancewa haka,” in ji Tinubu. “Nijeriya na adawa da keta ‘yancin addini, kuma ba ta goyon bayan hakan.”

Tinubu ya kara jaddada cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya yana kare ‘yan ƙasa masu bin kowane irin addini, tare da bayyana aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka da sauran ƙasashen duniya domin ƙarfafa fahimta da haɗin kai wajen kare al’ummomin addinai daban-daban.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#