Makaman sararin samaniyar Saudiyya sun kakkaɓo makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa a yankin tsakiya da gabashin ƙasar.

Tarkacen makamai masu linzami na ‘yan Houthi ya jikkata mutum 4, ya lalata gidaje 15 a Saudiyya

Mutane huɗu sun jikkata, yayin da gidaje 15 suka lalace bayan tarkacen makamai masu linzami guda biyu da aka kakkaɓo sun faɗo a wasu unguwanni a Riyadh, babban birnin Saudiyya, a cewar hukumomi.

Hukumar Kare Fararen-Hula ta Saudiyya ta sanar da cewa an kakkaɓo makaman masu linzami da mayaƙan Houthi suka harba a ranar Talata. Tarkacen da suka faɗo sun jikkata mata biyu da wani mutum da kuma yaro ɗaya.

Nan-take aka tura jami’an agajin gaggawa domin ba da taimakon lafiya da kuma tabbatar da tsaron wuraren da lamarin ya shafa.

A wata sanarwa ta daban, mai magana da yawun rundunar ƙungiyar haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya, Turki al-Maliki, ya tabbatar da cewa dakarun tsaron sama sun tare tare da lalata wani makami mai linzami da aka harba zuwa Al-Kharj, kudu maso gabashin Riyadh.

An kai hari Aramco

Sabbin hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da aka kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin samar da makamashi.

Ma’aikatar Makamashi ta Saudiyya ta bayyana cewa an kai hari kan wani ginin gudanar da ayyuka mallakin kamfanin mai na ƙasar, Saudi Aramco, a birnin Dhahran da ke gabashin ƙasar, a yammacin ranar Talata, lamarin da ya haddasa gobara.

Jami’an agajin gaggawa sun yi hanzarin shawo kan gobarar, kuma hukumomi sun ce babu wanda ya rasa ransa a harin.

Hare-haren na daga cikin wani farmaki da aka tsara, wanda ya shafi iyakokin ƙasar.

Rundunar haɗin gwiwar ta tabbatar da cewa ta kakkaɓo tare da lalata makamai masu linzami guda shida da jirage marasa matuƙa guda shida a ranar Talata.

Al-Maliki ya ce tsarin tsaron sama ya tare wasu makamai da ke kan hanyarsu ta zuwa Haradh da Dhahran, inda tarkacen da suka faɗo suka sauka a wasu unguwanni.

An kuma kakkabo jirage marasa matuƙa guda uku a arewacin Riyadh, tare da wasu hare-hare da aka daƙile a kudancin Saudiyya.

Barazanar mayaƙan Houthi

Hare-haren ta sama sun biyo bayan barazanar da mayaƙan Houthi suka yi a safiyar ranar Talata, inda suka ce za su kai hari kan hedkwatar Aramco da ke Dammam da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Sarki Khalid a Riyadh, da kuma matatar man Aramco da ke Riyadh.

Mayaƙan sun ce za su kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren sama da rundunar haɗin gwiwar ta kai kan wuraren da suke amfani da su a birnin Sanaa, babban birnin Yemen.

A martaninta, rundunar haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ta sanar da gudanar da wani “aikin soji na musamman” da nufin lalata hanyoyin samar da kayayyaki da kayan aikin da ke tallafa wa hare-haren mayaƙan Houthi.

Kwamandan Rundunar Sojin Haɗin Gwiwar ya bayyana cewa mayaƙan Houthi na amfani da wasu gine-ginen fararen-hula wajen adana kayayyakin soja.

A cewar rundunar, hare-haren sun shafi ma’ajiyar kayayyakin soja ta al-Sabaha da ke Sanaa, wuraren adana man fetur a ƙarƙashin ƙasa, da kuma wuraren sauke kaya daga jiragen ruwa a Al Hudaydah, da Sanaa da kuma Dhamar.

#