Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wani jirgin dakon kaya na Turkiyya ƙirar C-130 wanda ke kan hanyarsa daga Azerbaijan zuwa Turkiyya ya faɗi kusa da kan iyakar Azerbaijan da Georgia.
Ma’aikatar Tsaron Turkiya ta ce sojoji 20 sun yi shahada sakamakon hatsarin jirgin sama na dakon kaya na sojin Turkiyya a Georgia ranar Talata.
"Da misalin ƙarfe 06:30 na safiya (ƙarfe 02:30 agogon GMT) tare da haɗin gwiwar da hukumomin Georgia, aikin bincike da kuma tawagar masu bincike sun fara bincike kan tarkacen jirgin sojin na dakon kayan da ya faɗi a kan iyakar Azerbaijan da Georgia," kamar yadda ma’aikatar ta bayyana ranar Laraba.
Wani jirgin dakon kayan soji na Turkiyya ƙirar C-130 ɗauke da jami’an soji 20 ya yi hatsari kusa da Azerbaijan a kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya.
Ma’aikatar ta kuma fitar da sunayen dukkan sojoji 20 da hatsarin ya kashe.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi tattaunawa ta waya ranar Talata da takwaransa na Azerbaijan Ilham Aliyev da kuma takwaransa na Georgia, Firaiminista Irakli Kobakhidze domin nazari kan abin da ya faru a baya bayan nan game da ayyukan bincike da ceto.
Da yake magana a wani taro a babban birnin ƙasar Ankara, Shugaba Erdogan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka yi shahada.
Wasu ƙasashe da shugabanni daga sassan duniya sun miƙa saƙonninsu na jaje da ta’aziyya ga Turkiyya bayan hatsarin.
Comments
No comments Yet
Comment